Hukumar Albarkatun Mai (DPR) ta rufe gidajen mai biyar a Jihar Katsina saboda sayar da fetur sama da farashin da Gwamnatin Tarayya ta amince na N165 kowace lita.
Shugaban Gudanarwar DPR, reshen Jihar Katsina, Injiniya Mohammed Abdulrahaman ne ya jagoranci aikin duba yadda gidajen mai ke sayar da man fetur.
- Fyade: Gwamnatin Tarayya ta karrama matashiyar Kano da ta kirkiro manhaja
- Bakuwar cuta ta kashe mutum 2, wasu 160 na asibiti a Kano
- COVID-19: Najeriya ta aminta da rigakafin AstraZeneca da kasashe 13 suka dakatar
- An rufe makarantun Birnin Gwari bayan garkuwa da daliban firamare
“Muna sanya ido don tabbatar da gidajen mai sun bi umarnin da gwamnati, kuma duk gidan man da aka samu ya yi karin farashi za a rufe shi har sai ya bi dokar da aka gindaya.
“Kawo yanzu mun rufe gidajen mai biyar; hudu daga ciki an same su da laifin kara farashin mai, daya kuma suna sayar wa ’yan bumburutu.
Ya kara da cewa, gidan man suna sayar da mai cikin dare, da rana kuma sai nuna cewar ba su da shi, wanda a cewarsa hakan ya saba da doka.
Kazalika, ya ce DPR ba za ta gaza ba har sai ta tabbatar da gidajen mai na sayar da lita a kan N162 zuwa N165.
Abdulrahman, ya kara da cewa gwamnati na da tsare-tsare da mutane za su iya amfana wajen sayen man fetur cikin sauki a kuma farashi mai rahusa.