✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsabtace hakora ko baki

Yana da muhimmanci ga mace, har da namiji su rika kula da bakinsu. Domin gudun kada hakora su lalace ko kuma baki ya rika yin…

Yana da muhimmanci ga mace, har da namiji su rika kula da bakinsu. Domin gudun kada hakora su lalace ko kuma baki ya rika yin wari.Yawanci hakora sukan lalace ne tun mutum yana yaro, sakamakon sakaci da iyaye suke yi na sakar wa yaro kula da bakinsa.Yana da kyau iyaye su rika taimaka wa yaro wajen kula da bakinsa sosai.Kuma su ma su yi hattara da kula da nasu bakin.

Ga hanyoyin da suka kamata a kula da hakora:
• A samu burushi mai kyau,ba mai tauri ba, kuma kada ya cika laushi,wato dai-dai gwargwado.
• Idan an tashi daga barci sai a kuskure baki, bayan an ci abinci kuma sai a yi burushi. Saboda duk wani abinci da ya makale ya fita. Domin wannan abinci da yake makalewa a cikin hakori yana taimakawa wajen bata hakori.
• A rika wanke kan harshe da burushi sama-sama.
• Kada a yawaita cin kayan zaki koda yaushe.
• Duk lokacin da aka ci abinci ko aka sha wani abin zaki, a kuskure baki da kyau.
• Kada a rika cin kankara ko shan ruwa mai matukar sanyi.
• Duk lokacin da mutum zai kwanta barci da daddare ya goge bakinsa da burushi da man wankin baki.
• Kuma yana da kyau a rika amfani da aswaki wajen goge baki, domin yana kara karfin hakori,kuma yana sanya hakora su kasance koda yaushe cikin fari da haske.