Shugaban Kasar Amurka Donald Trump, ya kori Sakataren tsaronsa Mark Esper, matakin da ya sake jefa gwamnatinsa cikin rudani bayan wanda ta tsinci kanta a ciki na ki fadin amincewa da kayen da abokin hamayyarsa na jam’iyyar Democrat Joe Biden ya yi masa a zaben shugabancin kasar.
Mista Trump ya bayyana matakin hakan ne cikin wani sako da ya wallafa ranar Litinin a shafinsa na Twitter.
- CBN ya kalubalanci cire rubutun Ajami a kan Naira
- A wadata kowace kasa da rigakafin Coronavirus — Buhari
Ba tare da bayyana dalilin korar sakataren tsaron ba, Shugaba Trump ya gode masa kan yadda ya jajirce wajen rikon mukamin tare amboto Christpher Miller, Shugaban Cibiyar yaki da ta’adddanci ta kasar a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
Korar da aka yiwa Esper wanda ya yi sabani da Shugaba Trump kan shawararsa ta yin amfani da dakarun soji wajen kwantar tarzoma a kasar, na zuwa ne mako guda bayan zaben shugabancin kasar wanda aka gudanar a ranar 2 ga watan Nuwamba.
Har yanzu dai Shugaba Trump yana na a kan bakansa ta cewa an yi magudi a zaben, inda Babban Antoni Janar na Amurka, Bill Bar ya bayar da izinin fara bincike kan zargin aikata ba daidai ba a zaben.