✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Trump ya gurfana a gaban kotun Amurka

Sai dai duk da haka, ya ce zai tsaya takara a zaben badi

Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, ya gurfana a gaban wata kotun tarayya da ke birnin Miami na Jihar Florida don ya fuskanci zarge-zargen da ake masa.

Ana dai zargin tsohon shugaban ne da wasu jerin tuhumce-tuhumce har guda 37 masu alaka da boye wasu muhimman takardu, zamanin da yake mulki.

Sai dai yayin zaman kotun na ranar Talata, cincirindon magoya bayansa ne suka taru a wajen kotun don nuna goyon bayansu gare shi.

Amma an jibge tarin jami’an tsaro a kewayen kotun, inda aka hana magoya bayan nasa da ma sauran jama’a shiga ciki saboda tsaro.

Trump, wanda ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa neman shugabancin kasar a zaben shekara ta 2024 mai zuwa, ya sha bayyana shari’ar da ake yi masa da bi-ta-da-kulli.

Ana dai sa ran zai yi jawabi ga magoya bayansa da yammacin Talata a Bedminster da ke birnin New Jersey, bayan kammala zaman kotun.