Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce dole ne su kwato kasar daga hannun wadanda ke jagorantar ta a yanzu.
Trump ya ce al’ummar kasar su tsumayi sanarwa ta musmaman da zai fitar ranar 15 ga watan Nuwamba.
Ya ce zai bayyana sanarwar tasa ce a gabar tekun shakatawar Mar-a-Lago da ke Florida.
Tsohon shugaban ya ce jam’iyyarsu ta Republican a shirye take ta kwace Majalisar Tarayyar kasar a zabukan da za a gudanar.
“Za mu kwace Majalisu, da ma kasar baki daya kuma a 2024 mu za mu sake shiga fadar White House mai daraja,” in ji shi.
Trump na wannan jawabin ne kwana guda gabanin zaben ’yan Majalisar Wakilai da na Dattawa da kuma yanke muhimman shawarwari kan kujerun gwamnoni, da muhimman mukamai.
Kalaman nasa sun haifar da jita-jitar cewa zai sake tsayawa takara a 2024, duk da bai fito karara ya bayyana hakan ba a hukumance.