✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tottenham za ta iya lashe Kofin Firimiya a bana – Guardiola

Kocin Kulob din Manchester City da ke Ingila Pep Guardiola ya ce da alama kulob din Tottenham ne zai lashe gasar Firimiya ta bana a…

Kocin Kulob din Manchester City da ke Ingila Pep Guardiola ya ce da alama kulob din Tottenham ne zai lashe gasar Firimiya ta bana a Ingila, bayan ya lallasa na Manchester City da ci 2-0 a ranar Lahadin da ta wuce.
Guardila ya ce ganin yadda ’yan kwallon Tottenham suka murza leda da hakan ya sa suka yi wa na City kaca-kaca a wasan ya sa ya bayyana cewa da alama kulob din zai iya lashe gasar Firimiya a bana.
Sai dai ya nuna ’yan kwallon na Tottenham mafi yawansu sun kasance tare a tsawon shekaru biyu zuwa uku ba kamar ’yan kwallon City ba.
“Mun yi wasa ne da ’yan kwallon da suka kasance tare a tsawon shekara biyu zuwa uku tare da hakan ya sa suka fahimci juna fiye da ’yan kwallon City”, inji Pep Guardiola.
Sai dai Guardiola ya nuna su ma ’yan kwallon City ba kanwar lasa ba ne domin komai zai iya faruwa a yunkurinsu na lashe gasar Firimiyar ta bana.
Kawo yanzu Manchester City ce take saman teburin gasar da maki 18 a wasanni bakwai yayin da Tottenham take matsayi na biyu da maki 17 a wasanni 7.