Tsohon mai bai wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawara kan al’amuran Majalisar Wakilai, Abdulrahman Kawu Sumaila, ya ce sabuwar kungiyar siyasar nan ta TNM za ta sama wa ‘yan Najeriya mafita a 2023.
Kawu, wanda tsohon dan Majalisar Wakilai ne, ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, yana cewa siyasar Najeriya na bukatar kungiya irin TNM.
- DAGA LARABA: Yadda labaran karya ke buya a tsakanin al’umma
- DAGA LARABA: Yadda labaran karya ke buya a tsakanin al’umma
“Ina goyon bayan wannan tafiya saboda za ta farfado da dimokuradiyya, [ta kuma samar da] shugabanci na gari, ci gaba da sauran manyan nasarori”, inji shi.
Kazalika, Kawu ya ce zai goyi bayan duk wata tafiya da za ta karfafa dimokuradiyya kafin babban zaben 2023, ba tare da la’akari da bambancin ra’ayin da ke tsakaninsa da wasu ba.
Tsohon dan majalisar ya kara da cewa wadanda suka kirkiri tafiyar ta TNM mutane ne da ke da tarihi da kwarewa a fagen siyasa.
“Wadanda suka kirkiri wannan tafiya ta TNM da tsarinta sun shirya sosai.
“Ina murna saboda yawancinsu suna da gogewa a harkar siyasa,” inji tsohon dan majalisar.
Masu sharhi a kan al’amuran siyasa dai na ganin zai yi wuya a samar da wata kungiyar siyasa a wannan lokacin har ta yi tasiri a zabukan 2023.
Ko gabanin zabukan 2019 ma wasu jigajigan ”yan siyasa sun yi yunkurin samar da wata tafiya da juya akalar siyasar Najeriya, amma daga karshe ba ta sake zane ba.