✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tirela ta murƙushe mutane 25 a Ibadan

’Yan Arewa 18 na daga cikin mutane 25 da tirelar ta murƙushe

Wani hatsarin mota ya laƙume rayukan ’yan Arewa 18 da wasu mutane 7, a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Hatsarin da ya laƙume rayuka 25 a ranar Talata, ya auku ne a daidai mararrabar Agbowo Ajao a kan babbar hanyar Oyo zuwa Iwo.

Wani da lamarin ya auku a kan idanunsa ya ce burki ne ya ƙwace daga direban wata tirela da ke ɗauke da banduran kwanukan rufi inda a nan take ya danne wasu ƙananan motoci uku masu ɗauke da fasinjoji a cikinsu.

Sarkin Hausawan Ojo Tudun-Sunnah da lamarin ya auku a kusa da Fadarsa, ya shaida wa Aminiya cewa “a binciken da muka gudanar mun gano cewa ɗaya daga cikin motocin da haɗarin ya rutsa da su wata motar bas ce mai ɗaukar mutane 18 da ta taso daga Jihar Jigawa a kan hanyar zuwa Legas.”

Sarkin Hausawan ya ce duka fasinjoji 18 da ke cikin wannan motar bas sun gamu da ajalinsu.

Ya ce, “yanzu haka al’ummar Hausawa a nan Ojo Tudun-Sunnah sun taimaka da kudin sayen likkafani domin suturta waɗannan ’yan uwa Musulmi da za a yi masu jana’iza da binne su a makabartar Akinyele inda aka saba binne musulmi ’yan Arewa da suka riga mu gidan gaskiya.”

Binciken Aminiya ya nuna cewa sauran mutanen da ke cikin kananan motocin da tirelar ta murƙushe an kwashe gawarsu zuwa Asibiti.

Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto babu wani bayani a hukumance da aka samu dangane da wannan hatsari.

Sai dai binciken ya nuna cewa kafin isowar jami’an tsaro an ga jama’a suna kai ɗauki domin ceton waɗanda suka samu raunuka a wajen hatsarin.