Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokoki, Alhassan Ado Doguwa, ya ce kamun ludayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, irin na Buhari ne a bangaren ayyuka.
Doguwa ya bayyana haka ne tattaunawar da shirin Daily Politics na gidan talabijin na Channels ya yi da shi a daren ranar Talata.
- DAGA LARABA: Yadda Talla Ke Bata Rayuwar Yaran Arewa
- Qatar 2022: Yadda Faransa da Maroko za su barje gumi
“Bola Ahmed Tinubu zai karbi mulki daga wajen Shugaba Buhari kuma zai dora a kan ayyukan alheri da (Buhari) ya bari, don Buhari ya yi iyakacin abin da zai iya.
“Aiki ne wanda a sannu-sannu ake cim ma nasara,” a cewar Doguwa.
Sai dai ya ce shekaru takwas na mulkin Buhari ba za su ba shi damar gyara barnar da jam’iyyar PDP ta haddasa cikin shekara 16 ba.
“Idan ana magana a kan ilimi ne, misali, tun daga kan firamare, fakandare zuwa jami’a, tabbas za mu ce an samu ci gaba da tagomashi sosai.
“Magana ta gaskiya ita ce a shekara hudu ko takwas Muhammadu Buhari ba zai iya kawo karshen barnar da PDP ta yi ba.
“Muna bukatar fin shekara takwas, amma mun samu wani Buhari, jajirtacce wanda ya san makamar aiki.”
A bangaren tsaro, Alhassan Doguwa ya ce “An samu ci gaba sosai,” duk da cewa abin ya fi addbar mutane a yakin Arewa Maso Yamma.