Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dokokin Tarayya domin karɓo bashin $800 miliyan daga Bankin Duniya.
A wasiƙun da ya aikewa Majalisar Dattawa da Majalsar Wakilai, shugaba Tinubu ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ce ta amince da ciwo bashin domin ragewa talakawa raɗaɗin tattalin arziki.
Shugaban Majlisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio da shugaban Majalisar Wakilai Tajuddeen Abbas ne suka gabatar da wasiƙun a zaurakun majalisun a ranar Alhamis.
Shugaba Tinubu ya ce za a yi amfani da kuɗin ne wurin rabawa iyalai miliyan 12 tsabar kuɗi N8,000 a kowanne wata har tsawon watanni shida.
Ya ce za a rabawa mabuƙatan kuɗin ne kai tsaye ta asusun ajiyarsu domin tabbatar da cewa talakawa ne kawai suka amfana da tsari.
Ya kuma ƙara da cewa raba tallafin zai bunƙasa tattalin arziki, cimaka, lafiya, da ilimin iyalan da za su amfana.