Shugaban Kasa Bola Tinubu a wannan Juma’ar ya sanar da sallamar manyan jami’an hukumomin da ke karkashin Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta Tarayya.
Cikin wata sanarwar da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya fitar, Shugaban Kasar ya kuma maye guraben manyan jami’an da ya sallama da sabbin naɗe-naɗe.
- Jadawalin Gasar AFCON 2023 da za a fafata baɗi a Ivory Coast
- Falasɗinawa fiye da 300,000 sun rasa matsuganansu a Zirin Gaza — MDD
Sabbin manyan jami’an hukumomin da aka naɗa sun haɗa:
Hukumar Yi wa Kamfanoni Rajista (CAC) — Hussaini Ishaq Magaji, SAN;
Hukumar Horar da Ayyukan Masana’antu (ITF) — Afiz Ogun Oluwatoyin;
Hukumar Bunkasa Sarrafa Sukari (NSDC) — Kamar Bakrin;
Hukumar Kula da Futon Kayayyaki (NEPZA) — Olufemi Ogunyemi;
Hukumar Bunkasa Fitar da Kayayyaki (NEPC) — Nonye Ayeni;
Hukumar Bunkasa Zuba Jari (NIPC) — Aisha Rimi;
Hukumar Kula da Yanayin Man Fetur da Gas (OGFZA) — Bamanga Usman Jada
Hukumar Bunkasa Kananan da Matsakaitan Sana’o’i (SMEDAN) — Charles Odii.
Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki (SON) — Ifeanyi Chukwunonso Okeke;
Hukumar Kula da Bayanan Kudi (FRCN) — Rabiu Olowo;
Hukumar Kula da Musayar Kayayyaki (NCE) — Anthony Atuche, CFA;
Kasuwar Baje-Koli ta Kasa da ke Legas (LITFCMB) — Veronica Safiya Ndanusa;
Hukumar Kula da Dandalin Tafawa Balewa (TBSMB) — Lucia Shittu
Hukumar Bunkasa Kirkira da Zane-Zane (NADDC) — Oluwemimo Joseph Osanipin.