Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), kan sake buɗe matatar man fetur ta Warri bayan shafe shekaru ba ta aiki.
Ya bayyana ci gaban a matsayin abin da zai ƙara wa ‘yan Najeriya ƙwarin gwiwa.
- Masu son Abba ya tsaya da ƙafarsa za su cuce shi – Kwankwaso
- Sarkin Musulmi ya bayar da umarnin dubin watan Rajab
A cewar Bayo Onanuga, mai ba shi shawara na musamman kan yaɗa labarai, matatar a yanzu tana aiki wanda ke samar da ganga 125,000 a kowace rana.
Ya ce matatar za ta ƙara ƙarfin tace mai a cikin gida da kuma inganta tsaron makamashi a Najeriya.
Tinubu ya kuma yi kira ga NNPCL da su gaggauta gyaran matatar Kaduna da kuma matatar mai ta biyu da ke Fatakwal domin ƙarfafa matsayin Najeriya na jagora a harkar tace mai a Afirka.
Ya jinjina wa shugabancin NNPCL, ƙarƙashin jagorancin Mele Kyari, kan ƙoƙarinsu na farfaɗo da matatun mai na ƙasa.