Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin a taƙaita shagulgulan bikin Ranar ‘Yancin Kai na Nijeriya na bana da zai gudana a ranar 1 ga watan Oktoba mai kamawa.
Wannan shi ne karo na biyu ke nan a jere Gwamnatin Nijeriya tana ɗaukar wannan mataki la’akari da matsin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.
- EFCC ta kama tsohon Gwamna kan zambar N27bn
- Harin Offa: Kotu ta yanke wa ’yan fashin banki hukuncin kisa
A hirarsa da manema labarai yayin baje kolin shagulgulan da aka tsara gudanarwa a bana, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya ce Gwamnatin Shugaba Tinubu na sane kuma tana tausaya wa ’yan Nijeriya game da halin matsin tattalin arzikin da suke ciki, don haka aka taƙaita shagulgulan da za a gudanar a bikin.
An taƙaita shagulgula a bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kan Najeriya na 63 a bara, inda Sanata Akume, ya ce ba za a gayyaci shugabannin ƙasashen ƙetare ba, saboda halin matsin tattalin arzikin da ƙasa ke ciki.
A yayin ganawar ta jiya Alhamis, Akume ya ce an yanke shawarar ne a bisa la’akari da halin da ƙasa ke ciki, don haka Shugaba Tinubu ya amince a taƙaita shagulgula a bikin ‘yancin kan Nijeriya na 64.