✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya tallafa wa wadanda ambaliyar Jigawa ta shafa da N50m

Ya ce ya zama wajibi ya taka jihar kafa da kafa

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ba mutanen da iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a jihar Jigawa tallafin Naira miliyan 50.

Tinubu ya sanar da bayar da tallafin ne a ranar Talata, jim kadan bayan ya kammala yi wa Gwamnan jihar, Muhammad Badaru Abubakar, jaje a Dutse, babban birnin jihar.

Dan takarar ya kuma yi kira da a dada jajircewa da yin addu’a don ganin karshen ambaliyar a jihar da ma a kasa baki daya.

“Kodayake na mika jajena da kuma addu’a ga wadanda lamarin ya shafa ta hannun Gwamna, amma na ga cewa ya zama wajibi na tako kafa da kafa na jajanta muku, saboda zuwan nawa yana da muhimmanci,” inji Tinubu.

Yayin ziyarar dai, Tinubu ya sami rakiyar Gwamnan jihar Filato kuma Daraktan yakin neman zabensa, Simon Lalong da Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu da Shugabar Mata ta jam’iyyar, Dokta Betta Edu da kuma tsohon Shugaban EFCC, Malam Nuhu Ribadu.

Da yake mayar da jawabi bayan karbar Tinubu, Gwamna Badaru ya gode wa dan takarar saboda ziyarar.

Ya ce an sami ambaliyar ce a kwanakin baya a kananan hukumomin Kafin Hausa da Hadejia da Gumel da Malam Madori da Birnin Kudu da Gwaram da kuma Dutse. (NAN)