✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya kori shugaban ’yan sanda da na Kwastam, ya nada sababbi

Tinubu ya kori shugaban 'yan sanda da na Kwastam, ya nada sababbi

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabbin Manyan Hafsoshin Tsaron Kasa ba Babba Sufeton ’Yan Sanda da kuma shugaban Hukumar Kwastam ta Kasa.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ya fitar  ranar Litinin.

Sabbin wadanda aka nada din dai su ne Manjo Janar C.G Musa a matsayin Babban Hafsan Tsaron Kasa da Manjo T. A Lagbaja a matsayin Shugaban Sojojin Kasa, sai Riya Admiral E. A Ogalla a matsayin Shugaban Sojojin Ruwa, sai AVM H.B Abubakar a matsayin Babban Hafsan Sojojin Sama.

Kazalika, Tinubu ya nada DIG Kayode Egbetokun a matsayin mai rikon mukamin Babban Sufeton ’Yan Sanda na Najeriya, sai kuma Manjo Janar EPA Undiandeye a matsayin sabon shugaban leken asiri na sojoji.

Shugaba Tinubu ya kuma nada karin manyan hadimai guda biyu da kuma hadimai guda biyu.

Wadanda ya nada din su ne Hadiza Bala Usman da Hannatu Musa Musawa da Sanata Abdullahi Abubakar Gumel da Barista Olarewaju Kunle Ibrahim.

Tinubu ya kuma nada Adeniyi Bashir Adewale a matsayin sabon mia rikon mukamin Shugaban Hukumar Kwastam ta Kasa.

“A lura cewa wadanda aka nada manyan hafsoshin tsaro da shugaban ’yan sanda da na kwastam za su fara rike mukamamsu har zuwa lokacin da za a tabbatar musu da mukaman kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada,” in ji sanarwar.