Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi nasara a zaben shugaban kasa a Jihar Jigawa.
Baturen Zabe na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Armayau Hamisu na Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma ya ce dan takarar shagaban kasa na APC ne ya zo a matsayi na da.
- INEC ta ci gaba da tattara sakamakon zabe a Abuja
- Kabiru Gaya ya fadi zabe bayan shekara 16 a Majalisa
Wanda ya zo na biyu shi ne tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar sai kuma dan takarar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon Gwamnan Jihar Kano na Jam’iyyar NNPP a matsayi na uku.
Ya bayyana cewa APC ta samu kuri’u 421,390, LP 1,889, NNPP 98,234 sai PDP 386,587.