✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya ba kowacce jiha biliyan 5 ta rage radadin janye tallafin mai

Gwamnan Borno ne ya tabbatar da hakan a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta sanar da bayar da Naira biliyan biyar ga kowacce daga cikin jihohin Najeriya 36 da Abuja, domin su rage radadin janye tallafin man fetur.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa a Abuja ranar Alhamis.

Ya yi jawabin ne bayan kammala taron Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC), wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya jagoranta.

Mambobin majalisar dai sun hada da Gwamnonin Najeriya 36 da kuma Ministan Abuja da Ministan Kudi da Gwamnan Babban Bankin Najeriya da shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) da sauransu.

Taron dai ya tattauna batutuwa da dama ciki har da harkokin kudi na kasa da abubuwan yau da kullum da kuma raba tallafin rage radadin janye tallafin man da Gwamnatin Tarayya ta yi a karshen watan Mayu.

Daga cikin Gwamnonin da suka halarci taron akwai Gwamna Abdulrahman Abdulrazak (Kwara), Hope Uzodinma (Imo), Inuwa Yahya (Gombe) Dauda Lawal (Zamfara), Dr. Alex Otti (Abiya), Babajide Sanwo-Olu (Legas) da kuma Ademola Adeleke (Osun).

Sauran sun hada da Sanata Bala Mohammed (Bauchi), Uba Sani(Kaduna), Sheriff Obrevwori (Delta), Farfesa Charles Soludo (Anambra), Godwin Obaseki (Edo), Yahaya Bello (Kogi) da Umaru Namadi (Jigawa).

Kazalika, akwai Gwamna Umo Eno (Akwa Ibom), Bassey Otu (Kuros Riba), Lucky Aiyedatiwa (mai rikon mukamin Gwamnan Ondo), Dapo Abiodun (Ogun), Ahmad Aliu (Sakkwato), Agbu Kefas (Taraba), Abdullahi Sule (Nasarawa), Peter Mbah (Enugu) da Babagana Zulum (Borno).

Kazalika, Mataimakan Gwamnonin jihohin Katsina da Ribas da Yobe da Adamawa da Kano da Kebbi su ma sun halarci taron.