✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya ba da umarnin fito da kayan abinci daga rumbunan kasa

Idan ta kama ma za mu shigo da abinci daga ƙasashen wajen domin magance matsalar tsadar abincin.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin fito da kayayyakin abinci daga rumbunan da ke sassan kasar nan domin rage matsin da talakawa ke fuskanta a halin yanzu.

Ministan Labarai, Muhammad Idris ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja jim-kaɗan bayan taron gaggawa kan halin kuncin rayuwa da tsadar abinci da ’yan ƙasar ke fama da shi.

Ministan ya ce gwamnatin za ta fito da metric ton 42,000 na abinci daga rumbunan ma’aikatar harkokin noma.

“Ma’aikatar harkokin noma na da masara da gero da nau’in gari a rumbunan ajiyarta da ke sassan ƙasar daban-daban domin raba wa ’yan ƙasar nan ba da jimawa ba,” in ji ministan.

Ya ƙara da cewa gwamnati ta ji labarin cewa masu kamfanonin sarrafa shinkafa faɗin ƙasar na da tarin shinkafar da suka taskance, don haka gwamnati ta yi magana da su sun kuma amnce za su fito da metric ton 60,000, don a sayar wa ’yan ƙasar.

Ministan ya ce idan ta kama ma za su shigo da abinci daga ƙasashen wajen domin magance matsalar tsadar abincin da ake fama da ita.

“Nan gaba kaɗan za a yi haka idan ta kama a yi”, in ji Muhammad Idris.

Ministan ya gargaɗi ’yan kasuwa masu ɗabi’ar ɓoye kayan abinci alhali talakawan ƙasar na cikin matsin rayuwa, yana mai umartar da su buɗe shagunansu domin mutane su samu damar saya.

“’Ba abu ba ne na alkairi ana cikin wannan matsatsi, kai kuma ka je ka ɓoye abinci don wata manufa taka da daban, don haka gwamnati ke kira ga irin waɗanan ’yan kasuwa da su fito da waɗanan kayayyaki domin sauƙaƙa wa ’yan ƙasa”, in ji ministan.

Yana mai cewa duk ɗan kasuwar da ya ƙi bin wannan umarni to gwamnati ta san su ta kuma san matakin da za ta ɗauka a kansu.