✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tinubu ne ya fi kowa cancanta ya gaje ni —Buhari

Buhari ya ce ya zama dole jam'iyyar APC ta hada kai da dan takarar don cimma nasara a zaben 2023.

Shugaba Buhari ya bayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa da ya dace ya jogarnaci Najeriya.

Buhari, wanda ya taya Tinubu murnar lashe zaben fid-da dan takarar shugaban kasa da jam’iyyar APC ta kammala a ranar Laraba, ya ba wa Tinubu tabbacin samun cikakken goyon baya.

“Mun yi imani cewa Bola Ahmed Tinubu zai dora a kan kyawawan ayyukanmu da kuma nasarorin da muka samu a bangaren dimokiradiyya.

“Shi ne dan takarar da ya dace da fatar ’yan Najeriya saboda shi ne dan takarar APC kuma a karkashin gwamnatin jam’iyyarmu, Najeriya za ta iya cimma burinta a Afirka da ma duniya baki daya,” inji sakon da Buhari ya fitar ta hannun kakakinsa, Garba Shehu.

Tinubu dai shi ne dan takarar shugaban kasa da jam’iyyar APC, bayan ya lashe zaben fid-da gwanin da jam’iyyar ta kammala a ranar Laraba.

Buhari ya ce ya zama dole jam’iyyar APC ta hada kai da dan takarar don cimma nasara a zaben 2023.

Ya ce: “A matsayinsa na wanda ya yi nasarar a zaben fid-da gwani, yana da cikakken goyon baya ga mu.

“Yanzu, dole jamiyyarmu ta hada kai ta mara mishi bayan don cimma nasarar zaben 2023 domin gwamnatinmu za ta ci gaba da tabbatar da tsaron al’ummominmu, ta bunkasa tattalin arzikinmu kuma ya ci gaba da yaki da rashawa.