✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu na fifita Yarbawa da Kiristoci a naɗe-naɗensa — MURIC

Mun yi matukar mamakin yadda Tinubu yake nada Kiristoci da Yarabawa a manyan mukamai.

Kungiyar MURIC mai rajin kare martabar Musulmi a Najeriya, ta zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nuna son kai, a naɗe-naɗen da ya yi na mukaman gwamnati, tana mai cewa akasarin wadanda ya nada ‘yan kabilarsa ne da kiristoci.

Babban Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ne ya yi wannan korafi cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta yi nuni da muhimman nade-naden da shugaba Tinubu ya yi a kwanan nan a matsayin shaidar da ke tabbatar da zargin da take yi.

Sanarwar ta ce nade-naden da shugaba Bola Tinubu ya ke yi na nuni da cewa yana bai wa mutanen da suka fito daga bangaren da ya fito, wato kudu maso yammacin Najeriya fifiko ba tare da la’akari da sauran sassan kasar ba.

Kungiyar ta gargadi Tinubu, wanda ta zarga da tara ’yan kabilar Yarabawa da Kiristoci a gwamnatinsa,

Kungiyar ta yi kira a gare shi da dauki matakin da zai hada kan kasar, a maimakon wanda zai rarrabu kawunan al’umma.

“Mun yi matukar mamakin yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yake nada Kiristoci da Yarabawa a manyan mukamai tun farkon wannan gwamnati.

“Misali, biyar daga cikin manyan hafsoshin tsaro 8 da aka nada a baya Kiristoci ne, haka ma kuma ko a wajen nadin mukaman ministoci ba ta sauya zani ba.

“An yi watsi da dimbin hazikan Musulmi wadanda suka yi yakin neman zabe wajen tabbatar da cewa an kada wa tikitin Musulmi da Musulmi kuri’a a a lokacin zaben Shugaban kasa.

Ya ce, “Haka kuma, ko Farfesa Ali Isa Pantami wanda ya yi kwazo wajen jagorancin harkar sadarwa da fasaha a zamanin gwamnatin da ta shude, an yi watsi da shi.

“Haka kuma, abin takaici ne yadda aka watsa wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai kasa ido wajen nadin ministoci duk da cewa dai a karan farko ya nuna ba shi da ra’ayin mukamin.”

Nade-naden da Tinubu ya yi wadanda suka janyo tada jijiyoyin wuya dai, sun hada da shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ministan Kudi, Wale Edun Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Michael Cardoso da Shugaban Hukumar Tattara Haraji, Zacch Adedeji da sauran su.