Jam’iyyar APC mai mulki ta ce Gwamnatin Shugaba Tinubu ba ta da aniyar sauya tsare-tsarenta da manufofinta na kawo cigaban ƙasa.
APC ta kuma buƙaci babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi watsi da tunanin Tinubu zai sauya tsare-tsaren gwamnatinsa, tana mai kira ga jam’iyyar adawar ta hada hannu da gwamnati domin inganta rayuwar al’ummar Najeriya.
Ta kuma ƙaryata zargin da PDP ke mata na murɗe zaɓen gwamnan Jihar Edo da zummar mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya guda.
Idan ba a nanata ba Shugaban Kwamitin Amintattu na PDP, Sanata Adolphus Wabara, ya zargi APC da murɗe zaɓen na Edo a ƙoƙarinta na ganin mulki a Najeriya ya koma hannun jam’iyya ɗaya kacokan.