✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tim Cook ya sayar da hannun jarin Dala miliyan 750

Cook ya yi murnar cika shekara 10 yana jagorancin kamfanin Apple cikin nasara.

Shugaban Apple, Tim Cook, ya yi murnar cikarsa shekara 10 yana jagorancin kamfanin ta hanyar sayar da hannun jarin da kudinsa ya haura Dala miliyan 750.

Tim Cook ya sayar da hannun jarin ne bayan ya karbi kashi na karshe na alkawarin da aka yi mishi na kyautar hannun jari lokacin da ya gaji Steve Jobs a matsayin shugaban kamfanin mai kera wayoyin iPhone.

Daga lokacin da Mista Cook ya zama shugaban kamfanin a 2011 zuwa yanzu dai farashin hannayen jarin Apple ya rubanya fiye da sau 10 – hakan ne kuma ya sa ya cancanci kyautar hannayen jarin da aka yi alkawari.

Jaridar Financial Times ta ranar Asabar ta ruwaito cewa bayan cikar ka’idojin kyautar ranar 24 ga watan Agusta, an sayar da hannayen jarin Apple a kan Dala 148 zuwa Dala 150 kowanne daya, lamarin da ya sa Cook ya ci ribar Dala miliyan 752.

A wannan watan farashin hannun jarin Apple ya yi tashin gwauron zabo har ya kai Dala 151 kowanne.

Albashin miliyan uku

Yanzu haka dai jarin kamfanin na Apple ya kai Dala tiriliyan biyu da rabi – adadin da bai taba kaiwa ba a tarihinsa.

Asalin hannun jarin da aka yi wa Cook alkawari a 2011 na Dala miliyan 378 ne, lamarin da ya sa a lokacin ya shiga sahun shugabannin kamfanonin da suka fi samun kudi a Amurka.

A 2015 Cook, wanda kafar yada labarai ta Bloomberg ta ce ya mallaki abin da ya haura Dala biliyan daya a watan Agustan da ya gabata, ya ce zai kyautar da galibin dukiyarsa kafin ya mutu.

Mako guda da ya wuce Tim Cook, wanda ke karbar albashin Dala miliyan uku duk shekara, ya bayar da gudunmawar hannayen jarinsa a kamfanin Apple na Dala miliyan 10 ga kungiyoyin bayar da agaji.