Wata babbar motar dibar kasa ta take wasu ‘yan sanda biyu da ke kan hanyar su ta zuwa aiki a jihar Ekiti.
Lamarin ya faru ne a unguwar Adebayo, a garin Ado-Ekiti kan babbar titin Ado–Ifaki a ranar Litinin, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).
- An damke magidanci ya yi wa agolarsa ciki a Ekiti
- NAJERIYA A YAU: Yadda Aka Yi Cinikin Kuri’a A Zaben Ekiti
Wani wanda abin ya faru a idonsa ya fada manema labarai cewa, hatsarin na faruwa, direban tifaR ya sauka daga motar ya gudu.
A hirarsa da ‘yan jarida kan lamarin, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar, DSP Sunday Abutu, ya ce, ‘yan sandan na tafiya ne kan babur a hannunsu, yayin da mai tifar dibar kasar ya bar hannunsa ya kuma take su.
“Direban tiffar ya saki hannun nasa ne, sakamakon aiki da ake yi a kan hanyar, da hakan ta sa shi yin ratsen, har ta kai ya take ‘yan sandan biyu, kuma nan take suka rasu,” inji Kakakin.
Sunday Abutu ya kuma ce, an kama direban motar tifar bayan ya tsere, yayin da kuma a ka kai gawarwakin ‘yan sandan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Ekiti.
Babban Kwamandan Hukumr kKyaye Hadura ta Kasa (FRSC), Olusola Joseph ya yi kira ga direbobi da su daina guduN wace sa’a a duk lokacin da suke tuki, don gujewa aukuwar hatsari irin wannan.