✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tela ya rasu yana dinkin Sallah

A yammacin jajibirin Sallah, wato ranar Litini da ta gabata al’ummar garin Agege a Legas suka shiga jimamin rashin wani matashi mai sana’ar tela mai suna…

A yammacin jajibirin Sallah, wato ranar Litini da ta gabata al’ummar garin Agege a Legas suka shiga jimamin rashin wani matashi mai sana’ar tela mai suna Muhammad Auwal wanda Allah ya karbi rayuwar sa yana cikin dinka kayan sallah, bayan da ya fita hayyacinsa.

An yi jana’izar Marigayin da safiyar ranar Sallah kafin a yi karamar Sallar idi.

Muna fatan Allah ya jikansa ya baiwa ’yan uwan sa da abokan arziki hakurin jumre rashin.