✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taya ni mu gyara (3)

Ci gaba daga satin da ya gabata Ta wani bangaren kuma maigida ne yake shiga halin damuwa idan yana tare da matar da ba ta…

Ci gaba daga satin da ya gabata

Ta wani bangaren kuma maigida ne yake shiga halin damuwa idan yana tare da matar da ba ta son ta ji kukan ’ya’yanta.Domin kuwa duk tufkar da zai yi, sai ta warware.Don haka da wuya haka ta cimma ruwa. 

Wani lokaci kuma akan yi rashin sa a idan aka samu iyayen duk biyu ra’ayinsu ya zo daya wajen rashin son su bata wa yaransu rai.Domin akwai yaran da suke ba kwaba ba kyara.Duk abin da suka yi daidai ne.Za ka tarar yaro yana rashin ji da rashin kunya,amma sai iyaye su kawar da kai.Kuma babu wanda ya isa ya yi wa irin wadannan yara magana,sai su bata da iyayen.
Yadda za a shawo kan wadannan matsaloli kuwa shi ne,dole maza su samar wa iyalansu lokaci don zama da su.Su rika jawo iyalinsu jiki,musamman yara.Kuma su rika nuna musu muhimmancin karatu,wani lokaci ma su yi karatu tare,su rika koya wa yara abin da ba su sani ba.Ta haka ne kawai za su fuskanci alkibilar kowa.Sannan wajibi ne su sauke nauyin da Allah ya dora musu na yau da kullum,domin gudun jefa rayuwar iyali cikin kunci da halaka.
Su kuwa mata masu gallaza wa yaran da ba su ne suka haife su ba,yana da kyau su sani ba a yi wa yaro mugunta domin kuwa da na kowa ne. Allah ne kadai ya san wanda zai more shi.Kuma duk wanda ya yi da kyau, zai ga da kyau. Mugunta da hassada ba za su hana shi zama abin da Allah ya kaddara zai zama ba.Haka nan kuma kaddarar da ta faru ga wannan yaro ke ma za ta iya faruwa a kanki.Domin ko aure bai rabu ba, mutuwa za ta iya raba ki da danki ya shiga hannun wata matar ,kuma ba za ki so a gallaza wa danki ba.Don haka mata ku ji tsoron Allah ku sani “Zakaran da Allah ya nufa da cara,ko ana muzuru ana shaho sai ya yi”.
Su kuwa iyaye wadanda suke jin haushin juna lokacin da daya yake yi wa yaro fada,ya kamata ku sani yaro dai na kowa ne.Kuma duk a cikinku babu wanda zai so yaro ya lalace.Saboda haka a hadu a zama tsintsiya madaurinki daya.Kai maigida ka sani matarka da ’ya’yanka duk a wuyanka suke.Saboda haka ka taimaka wa matarka don a gudu tare a tsira tare.Matukar ba ta saka yaro aikin da zai cutar da shi ba, bai kamata ka rika hana wa ba.Idan mu ne yau, ai gobe ba mu ne ba.Ita ma mace ta daina goyin bayan yara a duk lokacin da mahaifinsu yake yi musu fada.Kamata ya yi ta goyi bayan maigida matukar a kan gaskiya yake fadan.Hausawa suna cewa “Ka ki naka duniya ta so shi,ka so naka duniya ta ki shi”.
Da fatan za mu hadu mu gyara domin ceto al’umma daga mawuyacin halin da suke ciki ===yawanci ya faru ne saboda sakaci da ake samu tun daga gida.