Ci gaba daga satin da ya gabata
Domin hatta abinci ba sa iya ba su ,sai dai wahala kala-kala ga duka ga zagi.Zancen makaranta kuwa bai taso ba,ko kuma ta tura su makaranta da yunwa ta yadda ba za su iya mayar da hankali su fahimci karatun ba.Sannan su dawo gida a bar su da yunwa.Kuma wani abin takaici shi ne yaro bai isa ya sanar da ubansa ba.Idan ya kuskura ya fada masa ,ba zai yarda ba ,wata kila ma ya kara shan duka a hannun uban,bayan wanda ya sha. Haka makota ma koda sun sani ba su isa su fada ba sai ya ce“ An saka wa iyalinsa ido”.Irin wadannan yara sukan shiga halin “Ni ’ya su”.Kwanan nan aka samu wasu yara guda uku da ’yar kimanin shekara 11 da ’yar shekara bakwai da dan shekara 5 suna watangaririya a tashar motar Zuba da ke birnin tarayya Abuja sun baro gidan mahaifinsu saboda gallazawar matar uba.Inda suka ce suna so su koma hannun mahaifiyarsu ne da ke zaune a kauyen Mariga ta jihar Neja.Wannan ba karamar barazana ba ce,domin yara za su iya bata ko su fada hannun mugu ko su shiga wata mummunar rayuwa da makamantan haka.
Wasu matan kuma suna tare da mijinsu, uban ’ ya’yansu amma sukan sha wahala kwarai idan suka hadu da mijin da ba ya so a taba ’ya’yansa.Domin akwai wata mata tana da ’ya’ya biyu mata, daya shekararta goma sha biyar,daya kuma shekararta goma sha biyu.Amma abin mamaki da takaici duk su biyun ba su iya girki da sauran aikace-aikacen gida ba.Wannan ya faru ne sakamakon duk lokacin da ta saka su aikin gida sai mahaifinsu ya hana su ,sai ya rufe ta da fada,ya ce “Me ye amfanin ’yan aikin da na dauko nake biyansu kudu”?In dai yana nan a gida ko kuma idan ya same su suna aiki to zai fara fada ya hana su.Saboda haka suka sangarce suka raina mahaifiyarsu, duk lokacin da ta saka su aiki sai su zama ba sa son yi har suka girma a haka ba su iya komai ba.Kuma ba ta isa ta yi musu fada ba sai ya hana.Wannan gata ne,ko cuta? A wannan yanayi ta yaya mace za ta samu kwarin gwiwar raino da dora yara a hanyar da ta dace?
Haka nan akwai wani shagwababben yaro dan kimanin shekara shida, shi ma ba shi da lafiya sai aka kwantar da shi a asibiti, sai mahaifin yaron ya hana uwar yaron zama,sai shi da kansa .Saboda yana ganin ba za ta iya kula da yaron yadda yake so a zuciyarsa ba.Domin ba ya kaunar ko kuda ya taba yaron nan.Sai likita ya zo don ya duba shi,sai kawai ya tsula wa likita fitsari a jikinsa ya bata masa kaya ,da likitan ya yi magana sai uban yaron ya ce ai likitan ne bai iya kula da yara ba, shi ya sa.Haka nan Nas ta zo wajen yaron kawai sai ya sa hannu ya mare ta. Ta yi magana uban ya maimaita abin da ya fada wa likita.Babu shiri likita ya sallame su daga asibitin,ya ce su rika zuwa ganin likita suna komawa gida.Daga jin wannan labari mai karatu ka san irin tabargazar da ’ya’yan wannan mutumin suke yi a gida ba sai an yi karin bayani ba.
Za mu ci gaba in sha Allah!