✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tauraruwar Arewa: Watan girmama matan Arewa ya tsaya

Aminiya za ta kawo muku bayanai game da wasu hazikan matan Arewa da suka zama ababen koyi

A sassa daban-daban na duniya ana daukar watan Maris na kowacce shekara a matsayin Watan Tunawa da Gudummuwar Mata a dukkan bangarorin rayuwa.

A lokaci irin wannan, akan yi abubuwa daban-daban don karrama mata da rawar da suke takawa wajen ciyar da al’umma gaba.

Wannan ne ya sa Aminiya ta ga ya dace ta karrama hazikan mata da suka jajirce wajen sauya rayuwarsu daga kasancewa ababen tausayi zuwa ababen misali, ababen alfhahri.

Wasu daga cikin wadannan matan kuma rayuwar al’umma suke fafutukar sauyawa ta hanyar bayar da gudummawa wajen kawo sauyi a rayuwar wasu — duk da cewa da dama daga cikinsu ba a ma jin labarinsu.

Tauraruwar Arewa

A tarihi, Tauraron Arewa (wato North Star, a Turance) wani tauraro ne da matafiya suke amfani da shi don gane inda suka dosa, musamman da dare.

Masana ilimin taurari sun ce shi wannan tauraro na Arewa ya fi sauran taurari da ke sararin samaniya haske.

Hakan ba zai rasa nasaba da abin da masana suka gano cewa Tauraron Arewa ba tauraro daya ba ne, wasu taurari uku ne da suke kurkusa da juna ake hango su a matsayin guda daya daga duniyar nan tamu.

Kasancewar matan da Aminiya take karramawa sun zama ababen misali da koyi, shi ya sa muka yi wa kowaccensu lakabi da “Taurauwar Arewa”.

A tsawon wannan wata na Maris za mu kawo muku tarihi da bayanan rayuwar wadannan mata a jaridar Aminiya da  shafukan Aminiya na intanet da kafofin sadarwarmu na zamani.

Ranar Mata ta Duniya

Bugu da kari, a ranar 8 ga watan Maris din ne ake bikin Ranar Mata ta Duniya.

A wannan rana za mu kawo muku bayanai da makaloli da hotuna da bidiyo da kuma hurarraki kai-tsaye a shafukan namu.

A kasance da mu a tsawon watan Maris a jaridar Aminiya da shafinmu na intanet, aminiya.dailytrust.com da kuma shafukanmu na Facebook da Twitter da kuma Instagram.