Ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu a Jihar Kano, sun bayyana talauci da tashe-tashen hankulan da ake fama da su a Najeriya a matsayin babban ƙalubalen da ke daƙile ci gaban mata.
Mataimakiyar Darakta a ƙungiyar da ke rajin Yaƙi da Talauci da Rashin Adalci a Duniya (Action Aid), Suwaiba Muhammad Ɗankabo ce, ta bayyana hakan albarkacin bikin Ranar Mata ta Duniya, da aka gudanar a dakin taro na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata a Kano.
- An ga watan Ramadan a Najeriya — Sarkin Musulmi
- Ramadan: Hukumar tace Fina-finai ta rufe gidajen gala a Kano
Ɗankabo ta ƙara da cewa samar da kyawawan manufofin gwamnati ne, kaɗai zai karfafi mata, da rage musu raɗadin tashe-tashen hankula da ya fi rutsawa da su, kasancewar su jigon al’umma.
“Ta mu gudummawar a matsayinnmu na ƙungiya mai zaman kanta, shi ne bayar da tallafin kayayyakin sana’o’in dogaro da kai na sama da Naira miliyan 40 ga mata da matasa 300 da aka horar a Jihar Kano,” in ji ta.
A nasa ɓangaren, Babban Daraktan Cibiyar Sasanta Rikice-rikice Da samar da Ci Gaba (DAG), Dokta Muhammad Mustapha Yahaya, cewa ya yi haɓaka rayuwar mace daidai yake da ciyar da al’umma gaba, kasancewar ita ce mai bayar da tarbiyya ga ‘ya’yan da za su zamo shugabannin gobe.
“Hakan na nufin samar musu da ingantaccen ilimi da sana’o’i, da kuma ba su damar damawa da su a kowane ɓangare a matsayinsu na ‘yan ƙasa.
“Wannan ne ya sanya a bana za mu horar da matan 1000 hanyoyin ƙarfafa zaman lafiya da hakuri da juna.
“Kuma za mu ci gaba da samar da hanyoyin kare su da yaranmu daga duk wani nau’in cin zarafi. Za kuma mu ƙarfafe su wajen ƙwatar haƙƙoƙinsu musamman waɗanda addinin Musulunci ya daɗe da tsare musu.”
Taken taron na bana shi ne ‘Zuba Jari don Samarwa Mata Ci gaba’.