✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: Hukumar Tace Fina-Finai ta rufe gidajen gala a Kano

Hukumar ta dauki mataki ne a shirye-shiryenta na tukarar watan azumin Ramadan.

Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta bayar da umarnin rufe gidajen gala a jihar, a shirye-shiryenta na tukarar watan azumin Ramadan.

Wannan na zuwa ne, biyo bayan wata ganawa da shugaban hukumar ya yi da jagororin kungiyar masu gidajen gala da ke jihar a ofishinsa.

A cewar shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, dokar za ta fara aiki ne daga ranar Lahadi har zuwa 1 ga watan Shawwal, wato ranar bikin karamar sallah.

El-Mustapha ya gargadi masu gidajen wasannin na gala da su guji karya doka domin duk wanda hukumar ta samu da laifin karya dokar, za ta dauki tsatstsauran mataki a kansa, ta hanyar soke lasisinsa.

El-Mustapha ya kuma gode wa shugabannin gidajen galar tare al’ummar Jihar Kano, dangane da hadin kan da suke bau wa hukumar a kowane lokaci.

Kazalika, ya ja hankalin al’ummar jihar cewa kofarsa a bude ta ke domin ba shi shawara ko sanar da hukumar duk wani al’amari da zai taimake ta domin samun nasarar ayyukan da ta sanya a gaba.