Amma shi Abu Dawud ya ce, Ukbata dan Amir ya ce, an ambaci camfi a wajen Annabi (SAW) sai Annabi (SAW) ya ce, “Abin da ya fi kyau shi ne kyakkyawar magana domin camfi ba zai mayar da Musulmi gida ba. Sai dai idan wani daga cikinku ya ga abin da zai dame shi to ga addu’ar da zai yi. Allahumma la ya’ti bil hasanati illa anta wala yadfa’us-sayyi’ati illa anta, wala haula wala kuwwata illa bika.” Ma’ana. (Ya Ubangiji babu mai zuwa da kyakkyawan abu sai Kai, kuma babu mai tunkude mummunan bala’i sai Kai. Babu karfi babu dabara sai daga wajenKa).
An samu Hadisi daga Ibn Mas’ud (RA) kuma daga Annabi (SAW) ya ce, “Yin camfi shirka ne” sau biyu. Ibn Mas’ud (SAW) y ace sai dai kowane daya daga cikinmu irin wannan tunanin yana faruwa da shi, sai dai dogaron da muka yi da Allah yana tafiyar mana da wannan kokwanton.
Imam Ahmad ya ji daga Ibn Umar (RA) ya ce Annabi (SAW), ya ce, “Duk wanda ya ga makaho ya ce, “yau babu sa’a ya koma gida, to wannan ya yi shirka.” Sai sahabbai suka ce to me zai kankare masa wannan laifin ya Manzon Allah? Sai Annabi (SAW) ya ce, ‘To ya yi wannan addu’ar. ‘Allahumma la khaira illa khairuka wala daira illa dairuka wala ilaha ghairuka.” Ma’ana: (Ya Ubangiuji babu wani alheri sai alherinka, babu wani camfi da zai cutar sai idan Ka yarda domin babu wani abin bauta na gaskiya sai Kai).
Shi kuma Fadlu dan Abbas ya ce abin da ake kira da camfi shi ne abin da ya tafiyar da kai ko ya hana ka tafiya.
Babi na Ashirin da Tara:
Kan taurari
Imam Bukhari ya ce daga kattada, “Allah ya hallici taurari ne domin abubuwa uku ado ne a sama, domin jifar shaidanu, kuma alama ce ga matafiya. Duk wanda ya yi musu wata fassara ba wadannan ba, to ya yi kuskure kuma ya yi hasarar aikinsa, ya kuma dora wa kansa abin da bai da ilimi a kai.”
Domin haka kattada ya ce makruhi ne sanin masaukan taurari. shi kuma dan Uyaina bai yi sauki ba a kan neman ilimin taurari ko da ba duba za a yi da su ba. Amma Ahmad da Is’hak sun ce in dai ba duba za a yi da su ba, to neman iliminsu ba laifi. Shi kuma Abu Musa Al-Ash’ari (RA) ya ce Annabi (SAW) ya ce “Mutum uku ba za su shiga Aljanna ba, wanda ya tsufa yana shan giya da wanda ya gaskata sihiri da mai yanke zumunci.” (Ahmad da Ibn Hibban suka ruwaito).
Babi na Talatin:
Rokon ruwa da taurari sihiri ne
Allah ya ce, “Arzikin da Allah ke saukarwa kuna jingina shi ga taurari alhalin kuma karya kuke yi.” (Waki’ah, 82). An samu Hadisi daga Abu Malik Al-Ash’ariyyi (RA) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Mutum hudu daga cikin al’ummata suna da siffa irin ta Jahiliyya har sai in sun tuba: “Fariya (alfahari) da dangi da sukar wata kabila da rokon ruwa da taurari da kuma kukan mutuwa.” An ce mace mai kukan mutuwa har in ba ta tuba ba kafin ta mutu, to za ta tashi Ranar kiyama da zani na dalma da riga ta bakin karfe ta wuta. (Imam Muslim ya ruwaito).
An samu Hadisi daga Zaidu dan Khalid (RA) ya ce, “Annabi (SAW) ya yi Sallar Asuba wata rana a wani waje da ake kira Hudaibiyya bayan an yi ruwan sama. Lokacin da aka kare Sallah sai ya fuskanci mutane ya ce, “Ko kun san abin da Allah ya ce? Sai suka ce, Allah da Manzonsa ne suka sani. Sai ya ce, Allah ya ce, “BayiNa sun kasu kashi biyu, wadansu sun yi imani da Ni wadansu kuma sun kafirce. Wanda ya ce an yi mana ruwa da falalar Allah da rahamarsa, to wannan ya yi imani da Ni, kuma ya kafirce wa taurari ke nan. Amma wanda ya ce an yi mana ruwa saboda tauraruwa kaza ta fito, to wannan ya kafirce Mini, ya yi imani da taurari.”
Ibn Abbas (RA) ya ce wadansu idan suka ga an yi ruwa sukan ce “Ai tunda tauraruwa kaza ta fito, shi ya sa aka yi ruwan nan don haka tauraruwa kaza ta yi gaskiya.” Domin wadannan camfe-camfe da suke yi ne Allah ya saukar da aya yana cewa, “Ai ba sai na rantse da musaukan taurari ba. Lallai shi Alkur’ani Littafi ne Mai girma. Domin an ciro shi ne daga Lauhil Mahfuz. Domin haka ba mai shafarsa sai masu tsarki, domin saukakke ne daga Ubangijin talikai. To ku wannan labarin na gaskiya kuke karyatawa, ku jingina arzikinku ga taurari? Lallai ku makaryata ne.” (Waki’a: 75-82).
Babi na Talatin da daya:
Ba a kwatanta son wani da son Allah:
Allah Ya ce, “Akwai daga cikin mutane wadanda suke son wadansu kamar yadda suke son Allah. Amma su muminai suna tsananin soyayya ga Allah ne shi kadai.” (Bakara: 165).
A wata ayar kuma Allah Yana cewa: “ka ce wa wadanda suka riki wani ba Allah ba, idan iyayenku ne kuka zaba wadanda su sun fi muku Allah, ko kuma ’ya’yanku, ko ’yan uwanku, ko matanku ko danginku, ko dukiyar da kuke tattalinta, ko jarin da kuke tsoron karyewarsa, ko gidajenku da kuka yarda da zama a cikinsu su ne kuka fi so a kan Allah da ManzonSa da kuma jihadi domin daukaka addinin Allah, to ku zauna ku jira har Allah ya zo da hukuncinSa.” (Tauba: 24).
Anas (RA) ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Imanin dayanku ba ya cika sai ya so ni fiye da yadda yake son dansa da iyayensa da sauran mutane baki daya.” (Bukhari da Muslim suka ruwaito). Kuma a wani Hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito, Annabi (SAW) ya ce, “Wanda ke da wadannan halaye uku ya samu dandanon imani. Ya zama Allah da MansonSa kawai yake so kuma ya so mutum don Allah; kuma ya ki komawa ga kafirci kamar yadda yake kin a jefa shi a cikin wuta.”
A wata ruwayar kuma Annabi (SAW) ya ce, ‘Mutum ba zai samu dandanon imani ba, sai ya so Allah da ManzonSa fiye da yadda yake son kowa, kuma ya ki komawa ga kafirci bayan Allah ya kubutar da shi kamar yadda yake kin a jefa shi a wuta.”
Ita kuma ruwayar Ibn Abbas (RA) ga yadda ta ce, “Wanda ya yi so domin Allah, ya kuma yi fushi domin Allah sannan kuma ya jibinci mutum domin Allah, ya kuma yi gaba domin Allah, to da wadannan siffofi ne zai samu yardar Ubangiji.” Bawa ba zai samu dandanon imani ba ko da sallolinsa da azuminsa sun yi yawa har sai ya zama kamar yadda aka fada. Hakika soyayyar mutane a nan ta zama domin wani abin duniya kawai. Don haka ko kiyama ta tashi masu soyayya irin wannan ba su da komai a wajen Allah. Shi ya sa Ibn Abbas (RA) ya ce irin wadannan mutanen su ne wadanda dangantaka ta yanke a tsakaninsu idan kiyama ta yi.
DSP Imam Ahmad Adam Kutubi
Zone 7 Police Headkuaters Wuse Zone 3,
Abuja, 08036095723