✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tauhidi ginshikin Musulunci (7)

Babi na Ashirin da daya: Yin shishshigi a kan kaburburan mutanen kirki yana mai da kaburburansu zama dagutu An samu Hadisi daga Imam Malik (RA)…

Babi na Ashirin da daya:

Yin shishshigi a kan kaburburan mutanen kirki yana mai da kaburburansu zama dagutu An samu Hadisi daga Imam Malik (RA) ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Allah kada Ka sanya kabarina ya zama gunki ana bauta masa, saboda hushin Allah ya  sauka a kan wadansu mutane da suka riki kaburburan Annabawansu masallatai.” Kuma dan Jarir, ya ji daga Sufyanu daga Mansur daga Mujahid ya ce, “Lata da Uzza sunayen wadansu mutane ne wadanda suke taimaka wa  alhazai idan sun je aikin Hajji suna ba su abinci da kwababben gari. To saboda wannan alheri da suke yi da suka mutu sai mutane suka rika rokon Allah a kaburburansu.” Haka Abu Jauza’i ya ce daga Ibnu Abbas (RA) ya ce, sun kasance ne suna kwaba wa alhazai gari. A wani Hadisi kuma Ibnu Abbas cewa ya yi, Allah Ya tsine wa mata masu ziyarar kabari da masu gina masallaci a kan kabari da kuma masu kunna fitillu a kan kabari. (Ahlu-Sunnan suka ruwaito) 

 Babi na Ashirin da Biyu: Shingen da Annabi (SAW) ya sanyawa tauhdi ya kuma toshe duk hanya da za ta kai mutane ga shirka:

Allah Ya ce: “Hakika Manzo ya zo muku daga cikinku. Kuma abin da kuke aikatawa na laifi yana yi masa zafi, kuma mai kwadayi ne a kan ku Musulunta. Amma dangane da abin da ya shafi muminai, mai tausayi ne, mai jinkai. Idan kuma kuka juya baya (kuka ki imani), to ka ce, ni na yi imani da Allah kuma Ya ishe ni komai, domin babu abin bautawa sai Shi, gare Shi na dogara, Shi ne Ubangijin Al-Arshi Mai Girma.” (Tauba:128).

Abu Huraira (RA) ya karbo wani Hadisi daga Annabi (SAW) yana cewa, “Kada ku mai da gidajenku kaburbura, kuma kada ku sanya kabarina wajen biki. Ku yi min salati, duk inda kuke salatin zai same ni.” (Abu Dauda ya ruwaito kuma masu ruwayar amintattu ne). Kuma Aliyu dan Husaini ya ga wani mutum yana zuwa kullum ta wata kofa kusa da kabarin Annabi (SAW) sai ya shiga ta wannan kofar yayi ta addu’a. Sai ya hana shi yin haka, ya ce, ko kana so in fada maka dalilin da na ji daga babana shi kuma daga kakansa shi kuma daga Annabi (SAW) “Kada ku sanya kabarina ya zama wajen kaiwa da komowa kuma kada ku sanya gidajenku su zama kaburbura. Ni dai ku yi min salati kawai duk inda kuke domin zai isa gare ni.” (An ruwaito daga wani littafi mai suna ‘Mukhtaratu’).

 Babi na Ashirin da Uku: Wadansu daga cikin wannan al’umma suna bauta wa gumaka Allah Madaukaki Ya ce: “Shin ba ka ga wadanda aka ba su rabo na littafi ba suna imani da sihiri da bokanci? Suna ce wa kafirai, ai kun fi jama’ar da sukacyi imani da Muhammad (SAW) shiryuwa?” (Nisa’i:51). A wata aya kuma Allah Yana cewa, “Kuna so in ba ku labarin abin da ya fi sharrin sakamako a wajen Ubangiji? (Su ne) wadanda Allah Ya la’ance su Ya kuma yi fushi da su kuma wadansu Ya mai da su birai, wadansu kuma aladu da kuma wadanda suka bauta wa wani ba Allah ba.” (Ma’ida: 60). A wata ayar kuma Allah Yana cewa dangane da samarin da suka shiga kogon dutse, “Wadanda suka yi rinjaye a kan al’amarin samarin da suka shiga cikin kogo sun ce, to tunda mun yi nasara, masallaci za mu gina a kan kabarinsu.” (Kahfi: 21).

Kuma Abu Sa’id abin da ya ce shi ne, Annabi (SAW) ya ce, al’ummarsa za ta yi koyi da Yahudawa kamar kibiya a cikin kwari (wato sawu da kafa). Kai har ma da za su shiga ramin damo, kuma za ku shiga. Sai sahabbai suka ce, su wane ne ya Rasulullah, kana nufin Yahudu da Nasara? Sai Annabi ya ce, su ne mana. (Buhari da Muslim suka ruwaito). Shi kuma Imam Muslim ga yadda ya ce, daga Sauban (RA), Manzon Allah (SAW) ya ce: “Allah Ya nuno min bangon gabas da na yamma, kuma Ya ce “Musulunci zai kai duk inda aka nuna min.” Ya ce kuma, “An ba ni taskoki biyu – fari da ja (wato Rum da Farisa). To ni da na ga haka, sai na roka wa al’ummata Allah kada Ka halaka al’ummata da yunwa, kuma Allah kada Ka dora kafiri a kan Musulmi har al’ummata ta hayayyafa. Nan take sai Allah Ya ce: “Na amshi addu’arka ya Muhammad. Idan ko na kulla hukunci ba wanda zai warware shi. Ni na ba al’ummarka abubuwa biyun da ka roka. Ba zan hallaka su da yunwa ba, ba kuma zan dora kafiri a kansu ba har su hayayyafa. Ko da kafiran da suke kewaye da su sun auka musu ba za su ci nasara a kansu ba. Amma ina iya dora kafiri a kan Musulmi idan suka ki jituwa har ya kai ga sashe suna kashe sashe, ko sashe yana bautar da sashe!” (Barkaniyyu ya ruwaito).

A wata ruwayar an kara da cewa domin Annabi (SAW) ya ce, “Abin da nake ji wa al’ummata tsoro, shugabanni masu batarwa. Idan takobi ya sauka a kan Musulmi, to ba za a daga shi ba. Kiyama ba za ta tashi ba har sai an samu wadansu jama’a daga al’ummata ta yi tarayya da Allah da wani, wadansu kuma su bauta wa gumaka. Za a samu makaryata talatin kowane yana cewa shi Annabi ne. To kada ku yarda da su. Domin ni ne cikamakin Annabawa, babu wani Annabi a bayana. Amma duk da irin wannan gumurzu wata jama’a daga al’ummata tana nan a kan hanya, Allah zai taimake ta ba abin da zai cutar da ita. Domin haka ne ma wadanda suka wulakanta ta ko suka tozarta ta ba zai dame ta ba har Allah Ya zo da hukuncinSa.”

Babi na Ashirin da Hudu: A kan sihiri

 Allah Madaukaki Ya ce, “Hakika wadanda suka koyi sihiri (ko bokanci ko duba) to ba su da wani rabo a wajen Allah (idan kiyama ta yi).” (Bakara: 102). Kuma Allah Ya ce, “Wadanda suke ba su da rabo su ne wadanda suke imani da bokanci da sihiri.” (Nisa’i: 51). 

Umar Bin Khattab (RA) ya ce, “Ma’anar ‘Jibti’ shi ne sihiri. Ma’anar ‘dagutu’ shi ne shaidanin malami wanda ke shiryarwa ba da Littafin Allah ko Hadisan Annabi (SAW) ba. Shi kuma Jabir (RA) ya ce, abin da ake nufi da ‘dagutu’ su ne bokaye ko ’yan duba wadanda Shaidan ke sauka gare su. Ga kowace kabila Shaidan yana sauka domin hallaka mutane. Shi kuma Abu Huraira (RA), cewa ya yi, Annabi (SAW) ya ce a nisanci abubuwa guda bakwai masu halakarwa. Sai sahabbai suka ce. “Ya Manzon Allah! Wadanne abubuwa ne masu halakarwa?” Sai Annabi (SAW) ya ce, “Shirka da Allah da sihiri da kashe rai wanda Allah Ya hana a kashe sai idan da wani dalilin shari’a da cin riba da cin dukiyar maraya da gudu ranar yaki da kafirai da kuma kazafi ga matar kirki, mumina kuma mai ibada.”

Jundub ya bayyana hukuncin mai sihiri wanda shi ne a fille kansa da takobi (Tirmizi ne ya ruwaito).

An samu wani Hadisi daga Buhari daga Bajalata dan Abdata ya ce: “Sayyidina Umar bin Khattab ya hukunta a kashe boka da bokanya.” Sai muka kashe mutum uku. Hafsa (matar Annabi SAW) haka ta yi hukunci domin ta sa an kashe wata kuyangarta da ta yi mata sihiri aka kuma kashe ta. Haka Jundub ya yi hukunci shi ma. Shi ma Ahmad haka ya ce, an samu daga sahabban Annabi (SAW) cewa hukuncin boka kisa ne.