Babi na Goma Sha Takwas
Shiriya ta Allah ce
Allah (SWT) Ya ce: “Hakika (Ya Muhammad) ba za ka iya shiryar da wanda kake so ba, sai dai Allah Shi ke shiryar da wanda Yake so. Shi ne Ya san shiryayyu.” (kasas:56). Dalilin saukar wannan ayar shi ne, an samu Hadisi daga dan Musayyib, shi kuma daga Babansa ya ce, lokacin da Abu Talib ya zo rasuwa, Annabi ya zo ya tsaya a kusa da shi. Akwai kuma wadansu kafirai biyu – Abdullahi Ibn Abu Umayya da Abu Jahal – a wajen. Sai Annabi ya ce, “Ya Baffana, ka ce ‘La’ilaha illal lahu’ mana in samu dalilin cetonka a wurin Allah”. Sai wadannan biyu da ke nan suka ce, “Yanzu za ka bar hanyar (addinin) Abdulmudallib?” Daga karshe dai Abu Talib ya ki ya ce ‘La’ilaha illal lahu.’ Duk da haka sai Annabi ya ce masa, “Zan nema maka gafara matukar ba a hana ni ba.” Sai Allah Ya saukar da ayar da Yake cewa: “Bai kamata ga Annabi da wadanda suka yi imani su nema wa mushirikai gafara ko da makusantansu ne.” (Tauba, 113). Sai wannan ayar kuma ta sauka game da Abu Talib, “Hakika kai (Ya Muhammad) ba za ka iya shiryar da wanda kake so ba, Allah Shi ke shiryar da wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya domin Allah Shi Ya san shiryayyu.” (kasas:56).
Babi na Goma Sha Tara:
Dalilin kafircin dan Adam a bayan kasa:
Dalilin kafircewar dan Adam a bayan kasa shi ne shishshigi a cikin addini, wato wuce iyaka. Allah Yana cewa, “Yaku wadanda aka bai wa Littafi! Kada ku yi shishigi a cikin addininku, kada kuma ku fadi wani abu ga Allah sai in gaskiya ne.” (Nisa’i: 171).
An samu Hadisi daga Ibn Abbas (RA) a kan dalilin saukar ayar da Allah Yake cewa: “Suka ce kada ku bar abubuwan bautarku. Kuma kada ku bar Wadda da Suwa’a da Yagusa da Ya’uka da Nasran.” Ibn Abbas ya ce wadannan sunayen mutanen kirki ne daga mutanen Annabi Nuhu (AS). Lokacin da suka mutu sai Shaidan ya yi musu wahayi a kan su yi mutum-mutuminsu su ajiye a wuraren zamansu da suke zama kuma su kira kowanne da sunayen wadannan mutanen kirkin. Suna zaton alheri ne, sai suka aikata haka, amma ba su bauta musu ba har sai da wadanda suka yi wadannan mutum-mutumin suka mutu. ’Ya’yansu da suka zo daga baya, sai suka manta dalilin da ya sa aka yi wadannan gumaka sai suka bauta musu.”
Ibnu kayyim, kuma ya ruwaito da kuma malamai da yawa daga cikin Salafus-Salih sun ce, lokacin da wadannan mutanen kirki suka rasu, sai ya zama ana ta roko a kan kaburburansu, aka kuma yi mutum-mutumin sai zamani ya yi tsawo. Da a ka manta dalilin yin su sai aka bauta musu. An samu Hadisi daga Umar, Annabi (SAW) ya ce: “Kada ku daukaka ni kamar yadda Nasara suka daukaka Isa dan Maryam. Ni bawan Allah ne, kuma idan kuna so ku yabe ni, ku ce “Bawan Allah kuma Manzon Allah.” (Buhari da Muslim suka ruwaito). Amma a wani Hadisi abin da Annabi ya ce shi ne, “Ku daina shisshigi domin abin da ya halakar da mutanen farko shi ne shisshshigi.” A wani Hadisi da Mas’ud ya ruwaito, Annabi (SAW) ya ce, “Masu shisshigi sun halaka.” Annabi (SAW) ya fadi haka har sau uku.
Babi na Ashirin
Hani ga bautar Allah a kan kabarin mutumin kirki, to yaya idan har aka bauta wa mutumin?
An samu Hadisi daga A’isha (RA) daga Ummu Salma. Ummu Salma (RA) ta ambata wa Annabi (SAW) labarin wani coci da ta gani a kasar Habasha saboda abubuwan da ke cikinsa na hotuna. Sai Annabi ya ce mata, “Ai halin wadannan mutane, idan wani mutumin kirki daga cikinsu ya rasu ko wani bawan Allah nagari sai su yi masallaci (wurin bauta) a kan kabarinsa su kuma yi hotonsa su makala a cikin masallacin. To wadannan mutane su ne mafiya sharrin bayi a wajen Allah.” Dalilin da ya sa Annabi (SAW) ya fadi haka, domin wadannan mutanen sun hada fitina biyu. Fatina ta daya, sun gina masallaci a kan kabari wanda yin haka bai halatta ba. Na biyu, sun yi gumakan wadannan mutanen suna bauta musu. Wannan shi ne fitinar da Yahudawa da Nasara suka auka cikinta. A wani Hadisin kuma, A’isha (RA) ta ce, lokacin da Annabi (SAW) yake cikin ciwon ajali yana da wani bargo wanda yake rufa da shi. Idan ciwon ya yi sauki sai ya rufa da bargon, idan kuma ya yi tsanani, sai ya yaye bargon ya ce “Haka nan Allah Ya tsine wa Yahudawa da Nasara saboda sun riki kaburburan Annabawansu masallatai (wuraren ibada).” Abin da ya sa Annabi (SAW) ya yi wannan magana saboda kada bayan rasuwarsa a gina masallaci a kan kabarinsa. Don haka ne ya tsawatar wa al’ummarsa kada su aikata haka. Domin haka ne sai A’isha (RA) ta ce, “Don haka ne ba a fitar da kabarin Annabi (SAW) daga cikin dakinta ba. Da ya rasu sai aka bizne shi a dakina. Ba domin haka ba, da an bizne shi a ‘Bakiyya’ inda ake bizne sahabbai.” (Buhari da Muslim suka ruwaito).
An samu Hadisi daga Muslim wanda Jundub dan Abdullahi (RA) ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) kafin ya rasu da kwana biyar ya ce, “Ku sani ni na kubuta daga Allah saboda ban riki wani daga cikinku badadina ba. Abin da ya sa ban yi haka ba, domin Allah Ya rike ni badadinSa kamar yadda Ya riki Annabi Ibrahim (AS) badadinSa. Da kuma har zan riki wani badadi daga cikin al’ummata, to da na riki Abubakar (RA). To ku sani, wadanda suke gabaninku suna gina masallatai (wuraren ibada) ne a kan kaburburan annabawansu. To ku kada fa ku riki kaburbura masallatai, domin yin haka haramun ne a Musulunci.” Domin haka ne Annabi (SAW) ya hana a yi masallaci a kan kabarinsa a karshen rayuwarsa. Sannan Annabi (SAW) ya yi tsinuwa. Saboda haka duk wanda ya aikata haka da wanda ya yi Sallah a kan kabari yana cikin wannan tsinuwar, domin A’isha (RA) ta ce, domin kada a je a rika Sallah a Bakiyya shi ya sa ba a kai Annabi (SAW) can ba. Kuma saboda su sahabbai ba za su gina masallaci a kusa da kabarin Annabi (SAW) ba, sai dai wani yana iya cewa sai ya je wajen zai yi Sallah. To idan ko ya yi Sallah a wajen, ya zama masallaci domin duk inda ake Sallah sunansa masallaci ko da ba a gina shi ba kamar yadda Annabi (SAW) ya ce, “An sanya min kasa tsarkakakkiya ce kuma wurin yin Sallah.”
Ahmad, ya samu Hadisi daga Ibn Mas’ud (RA) shi kuma daga Annabi (SAW) ya ce, “Wadanda suke mafi sharrin mutane, wadanda kiyama ta same su suna da rai da kuma masu gina masallaci a kan kaburbura.” (Abu Hatim ya ruwaito).