✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tauhidi ginshikin Musulunci (4)

 Babi na Goma Sha daya Ba a yanka domin Allah a wurin da ake yanka domin wanin Allah  Allah Ya ce, “kar ka je ka…

 Babi na Goma Sha daya

Ba a yanka domin Allah a wurin da ake yanka domin wanin Allah 

Allah Ya ce, “kar ka je ka yi sallah a wannan masallacin har abada, domin masallacin da aka gina shi a kan tsoron Allah tun ranar gininsa shi ya fi dacewa ka yi sallah a ciki domin akwai mazaje muminai a cikinsa wadanda ke kaunar su tsarkaka. Allah kuma Yana son masu son tsarkakuwa.” (Taubah, 108) 8

  Babi na Goma Sha Biyu

Shirka ne yin alwashi domin wanin Allah

Allah Ya ce, dagane da sha’anin muminai, “Su ne wadanda suke cika alwashinsu, kuma suna tsoron wata rana wacce take sharrinta mai fantsama ne”. (Al-Insan, 7). Amma awata aya sai Allah Ya ce, “Duk abin da kuke ciyarwa ko kuka yi alwashin bakance, hakika Allah masani ne a kansa.” (Bakara, 270).

An samu Hadisi daga A’isha (R.A) cewa Annabi (S.A.W) ya ce, “Wanda ya yi alwashin zai bi Allah to ya yi kok arin daurewa domin biyayaya ga Allah. Amma wanda yayi alkawarin zai sabawa Allah, to ya bari kar ya sabawa Allah din”. 

   Babi na Goma Sha Uku

 Neman tsari da wanin Allah shirka ne Allah Ya ce a cikin Alkur’ani, “wadansu mazaje daga mutane suna neman tsari daga wadansu mazaje na aljjanu. To yin haka sai ya kara wa aljannu girman kai.” (Jinn, 6). (Dalilin saukar wannan aya, Larabawa sun kasance idan sun yi tafiya mai nisa a cikin Sahara; idan kuma tafiyar ta kai su dare to idan suka samu inda za su yada zango, maimakon su kira sunan Allah sai su kira sunan aljani. Misali sai suce “Ya Ifritu ka karemu” ko “Ya Ra’asul Gaul’ da dai sauransu. Da aljannu suka ji mutane suna haka, sai suka dauka ashe mutane suna tsoronsu. Don haka sai wannan aya ta sauka domin nuna cewa neman tsari da aljannu shirka ne).    

Domin haka aka samu wani Hadisi wanda ya ce, idan mutum ya sauka wani waje yana jin tsoron wani abu domin kar ya cutar da shi sai ya ce, ‘ina neman tsari da kalmomin Allah baki dayansu, Ya tsare ni daga sharrin abin da Ya hallita’, to har ya tashi daga wajen ba abin da zai cutar da shi. (Muslim ne ya ruwaito).

 BABI NA GOMA SHA HUdU

  Neman agaji da sunan wanin Allah ko kiran wanin Allah shirka ne Allah Ya ce, “kar ka kira wanin Allah domin ba zai amfanar da kai komai ba kamar yadda ba zai cutar da kai ba. In kuma ka ce sai ka kira wani, don yin haka din neman taimako ne, to hakika kana cikin azzalumai. Idan Allah Ya sanya maka wata cuta, ba mai yaye maka sai Shi. Idan kuma Ya yi nufinka da wani alheri, ba wanda zai iya mayar da wannan alheri. Domin Allah Yana bada falalarsa ga wanda Yake so daga cikin bayinSa. Shi ne mai gafara mai jinkai”. (Yunus, 106 -107). Allah Ya ce dangane da masu kiran wani ba Allah ba: “Wadanda kuke kira koma bayan Allah, arzikin ku fa ba a hannunsu yake ba, ku nemi arzikin ku daga wajen Allah kuma ku bauta maSa, ku kuma gode maSa. Zuwa gareShi za ku koma.” (Ankabut, 17). Allah Ya sake cewa, ‘Ba wanda ya fi bacewa kamar mai kiran wanin Allah, wanda ko da ya tsaya yana ta kiransa har zuwa kiyama, ba zai amsa masa ba.” (Ahkaf, 5). 

Har yanzu dai Allah yana cewa dangane da masu kiran wani ba Allah ba, “Wane ne mai amsa addu’ar wanda ya shiga tsanani idan ya roke shi, ya yaye masa damuwarsa, kuma ya sanya ku halifu a bayan kasa? Shin akwai wani ne (abin bauta) tare da Allah?” (Namli, 62).

An samu wani Hadisi wanda ya nuna ba a neman taimako ga kowa sai Allah, wanda Imamu dabrani ke cewa, “An samu wani munafiki a lokacin Annabi da yake cutar da muminai. Ana kiransa Abdullahi Bin Ubayyi’bin Salul. Da sahabbai suka damu da cutarwarsa sai  suka ce, mu je wajen Annabi mu nemi agaji da shi domin ya shiga tsakaninmu da wannan munafiki. Sai suka je wajen Annabi suka ce, “Ya Manzon Allah, ka agajemu ka raba mu da wannan munafiki”. Sai Annabi (S.A.W) ya ce, “Ai ba’a neman agaji da ni. Wanda ake neman agaji da shi, Shi ne Allah, Mai Girma da Buwaya”.

 BABI NA GOMA SHA BIYAR

 Hani ga tarayya da wanin Allah:

Allah Yana cewa, “Shin za ku yi tarayya da wadanda ba su hallicci komai ba, (alhali) su aka hallita? Ba za su iya taimakawa kansu ba balle ma su taimakawa wasu”. (A’araf, 1911-1912). Allah kuma Yana cewa dangane da hani kan kiran wani, “Ku sani fa wadanda kuke kira koma bayan Allah ba su mallaki koda yanar cikin dabino ba (domin haka kar ku kira su). Idan ko kuka kirasu, to ba za su amsa kiranku ba. Idan ma sun ji kiran naku, ba za su amsa ba. Ranar kiyama kuma za su butulcewa tarayyar da kuka yi da su. Kuma ba mai iya ba ka labari irin labarin Allah.” (Fadir, 13).

An samu Hadisi sahihi daga Anas ya ce, an yi wa Annabi rauni a kai ranar yakin Uhud har aka karya masa daya daga cikin hakoransa na gaba. Sai Annabi ya ce, “Yaya wadannan mutane za su yi albarka bayan sun yi wa Annabinsu rauni?” Sai aya ta sauka ana fadawa Annabi cewa, “Al’amari ba a hannunka yake ba”. 

Shi kuma Ibn Umar (R.A) cewa ya yi ya ji Annabi (S.A.W) yana cewa, idan ya dago daga ruku’i a raka’ar karshe ta asuba, “Allah ka la’anci wane, Allah ka la’anci wane” bayan ya ce, “Sami Allahu Liman hamidahu, Rabbana wa lakal hamdu”. Sai Allah (S.W.T) Ya saukar da aya Yana cewa, “Al’amari ba a hannunka yake ba”. Amma wata ruwaya ta ce, Annabi yana kiran sunayensu yana cewa, “Allah Ka la’anci Sufwanu dan Umayya, Allah Ka la’anci Suhailu dan Amr, Allah Ka la’anci Harisu dan Hisham”. Sai aya ta sauka tana cewa, “Al’amarin ba a hannunka yake ba”. Shi kuma Abu Huraira ga abin da ya ce, ‘Annabi ya tashi a cikin jama’a lokacin da aya ta sauka wacce ke cewa “ka gargadi danginka na kusa”, sai ya kira kuraishawa baki daya ya ce, “ya ku kuraishawa” ko wata kalma mai kama da wannan, “ku fanshi kawunanku domin ni ba zan iya amfana muku komai a wajen Allah ba”. Sai ya kira Abbas (dan baffansa) ya ce, “Ba zan iya amfana maka komai a wajen Allah ba”. Sai ya kira Safiyya (‘yar uwar mahaifiyarsa) ya ce, “Ba zan iya amfanar maki komai wajen Allah ba”. karshe kuma sai ya kira ‘yarsa ya ce, “Ya Fatima, idan kina da bukata ta dukiya, ki tambaye ni abin da kike so. Idan ina da shi zan ba ki, amma ba zan iya amfana miki komai wajen Allah ba.”

BABI NA GOMA SHA SHIDA

 Abin da ke faruwa ga Mala’iku Idan Allah ya yi  magana  Idan Allah (S.W.T) Ya yi magana Mala’iku sukan tsorata har ma su suma. Domin haka ne Allah Ya ba da labari a cikin Suratul-Saba, “Idan aka zare wannan tsoron daga zukatansu (Mala’iku) sai su ce wa Jibrilu, ‘me Ubangji Ya fada?” Sai Jibrilu ya ce ‘Allah Ya fadi gaskiya, domin Shi Madaukaki ne, Mai Girma”. 

An samu Hadisi daga Abu Huraira, Annabi (S.A.W) ya ce, “Idan Allah Ya hukunta wani al’amari a sama, Mala’iku sai su fadi da fukafukansu don kaskantar da kai ga zancen Allah domin suna jin maganar kamar wata sarka ce aka ja a kan falalen dutse. Wannan karar tana sanya su suma har idan suka farka daga wannan sumar sai su ce ‘me ubangijinmu Ya fada?” Sai Jibrilu ya ce, ‘Allah Ya fadi gaskiya domin Shi ne Madaukaki, Mai Girma’. To a wannan lokaci ne aljannu masu satar ji suke satar ji, kuma su fada wa na kusa da su. Har ma lokacin da Sufwan yake siffantawa sai ya bude tsakanin yatsunsa, wani a kan wani ya ce haka suke yi. Watau na sama ya fadawa na kasa da shi har su fada wa boka ko dan duba. Shi kuma idan ya tashi zai fada sai ya kara karya dari. 

To amma, wasu aljannun kafin su kai labari, taurari suna kona su. Wadansu kuma suna isar da labarin har zuwa ga boka. Domin haka sai ya hada da wannan gaskiyar guda daya da karya dari. Idan idan ya fada musu (mutane) wannan gaskiya suka ga abin ya faru, to duk abin da ya fada musu sai su gaskata shi. Ko da wani zai karyata a cikinsu, sai wadansu su ce masa ‘ba ya fada mu na kaza ba kuma abin ya faru? Domin haka duk abin da ya fada gaskiya ne. Da haka suke gaskata bokaye. Amma ruwayar Nawwas dan Sam’ana (R.A.) ya ce, Annabi (S.A.W) ya ce, “Idan Allah Yana so Ya aiko da wani umarni, to sai Ya yi magana ta hanyar wahayi. Lokacin da Ya yi wannan maganar sai sama ta yi motsi mai tsanani don tsoron Ubangiji Mai Girma da daukaka. To, idan Mala’iku suka ji wannan magana ta Ubangiji sai su ma su fadi suna masu sujjada ga Allah. Farkon wanda zai daga kansa shi ne Jibrilu, sai Allah Ya fada masa sakon da Yake so Ya aike shi da shi da abin da Allah Yake so. Sai Jibrilu ya zo ya wuce Mala’ikun domin kai wannan sakon. Ko wacce sama ya zo zai wuce sai Mala’ikun saman su tambaye shi, ‘me Ubangijin mu ya fada ya Jibrilu?” Sai Jibrilu ya ce musu ‘Allah Ya fadi gaskiya domin Shi ne Madaukaki Mai Girma’. Sai Mala’iku baki dayansu su ce, “Allah Ya fadi gaskiya. Shi Mai Girma ne, Madaukaki’, har dai Jibrilu ya isar da wahayi ga wanda aka umurce shi da ya kai wa. 

BABI NA GOMA SHA BAKWAI

 CETO:

 Allah Ya ce, “ka yi gargadi da shi (Alkura’ni) ga wadanda suke tsoron a tada su gaban Ubangijinsu ba su da wani waliyyi koma bayan Allah, balle wani mai ceto, ko kwa ji tsoron Allah.” (An’am, 51). Amma a Suratul Zumar, Allah Ya ce, “Ceto baki daya naSa ne”. (Zumar, 44). A wata ayar kuma Allah Yana cewa, “Babu wani mai yin ceto a wajenSa sai da izininSa.” (Bakara, 255). A wata ayar Allah Yana cewa, “Da yawa mala’iku a cikin sama da kasa ba su da ikon ceton kowa sai bayan Allah Ya yi izini ga wanda Yake so, Ya kuma yarda da Shi.” (An-Najmi, 26). Allah Ya ce a wata ayar, “ku kira wadanda kuke kira koma bayan Allah wadanda ba su mallaki ko kwayar zarra ba a sama da kasa, kuma ba su da wani tarayya da Allah a sama da kasa, kuma ba su da wani mai taimako, kuma fa ceto ba zai yi amfani ba sai ga wanda Allah Ya yi wa izini”. (Saba, 22). (Wadannan ayoyi sun tabbata mana akwai ceto kenan bayan Allah Ya yi izini). Kamar yadda Abul Abbas Ibn Taimiyya ya fassara wannan ayar da ke cikin Suratul Saba ya ce: “Allah Ya kore duk wani abin da mushirikai suke hadawa da Shi. Na farko Allah Ya kore mulki ga waninSa, Ya kore rabo ga waninSa ko mai taimako gareshi. Allah Ya kore duk wadannan abubuwa guda uku sai Ya tabbatar da na hudu, shi ne ceto. Ya ce akwai amma ba zai yi amfani ba sai wanda Allah ya yi masa izini-kamar yadda ya zo a Suratul Ambiya’. “Ba za su yi ceto ba sai wanda Allah Ya yi masa izini”. (Ambiya, 28). 

To shi wannan ceto wanda masu tarayya da Allah suke cewa akwai shi korrare ne kamar yadda Alkur’ani ya bada labari. An ruwaito Hadisi daga Annabi (S.A.W) da cewa zai zo idan aka yi kiyama ya yi sujjada ya kuma gode wa Ubangiji. Shi ma Annabi da zai yi ceto ba da ceton yake farawa ba tukunna sai ya yi sujjada ga Allah sannan Allah Ya ce, “daga kanka ka fadi damuwarka, ana ji kuma ka roki abin da kake so an ba ka ka yi ceto ga wanda kake so ka ceta, an ba ka”. Domin tabbatar da wanda zai samu ceton Annabi sai Abu Huraira ya ce, “Wane ne zai samu cetonka ya Manzon Allah? Sai Annabi ya ce, “Wanda ya ce ‘La’ilaha illallahu’ kuma bai yi shirka ba”. To da wannan za mu gane cewa ceton Annabi yana nan, amma fa ga wadanda suka tsarkake aikinsu domin Allah Shi kadai, kuma sai da yardar Allah. Sannan wannan ceton ba ya kasancewa ga wanda ya yi tarayya ga Allah.

Hakikanin ceto, Allah ne Ya fifita wadansu bayinSa da shi wadanda suka yi sabo amma bai kai shirka ba, sai Allah Ya gafarta musu saboda addu’ar wanda aka yi wa izini domin Allah Ya girmama shi, Ya kuma samu matsayi abin yabo.

Ceton da Alkur’ani ya bayyana babu shirka a ciki. Domin haka ne ma ya tabbatar da ceton da izinin Allah za a yi a wurare da yawa. Kuma Annabi (S.A.W) ya bayyana cewa ceton ya takaitu ne ga masu tauhidi, wadanda suka tsarkake Allah da bauta.