To wannan ya ishi mai hankali wa’azi domin ya tuba zuwa ga Allah. Kuma ya nemi gafarar Ubangiji kan mummunan zaton da ya yi wa Allah. Kuma da zacka binciki duk wanda za ka bincika da za ka samu wani yanki na mummunan zato a zuciyarsa da kuma zargi a gare shi. Don haka idan wani abu ya same shi wanda ba shi ne yake nema ba, sai ya ce ‘Ai da na yi kaza da hasara ba ta same ni ba.’ Wani irin wannan kadan ne a zuciyarsa, wani kuma mai yawa, don haka kai mai karatu ka binciki kanka. Shin akwai musun kaddara a zuciyarka, ko kuma shin ka kubuta? Idan har ka kubuta to ka yi sa’a, idan ba ka kubuta ba, to ina tsoron ba ka da rabo a Lahira ke nan. Allah ya tsare mu.
Babi na Sittin: Hukuncin masu musanta kaddara:
An samu Hadisi daga Ibn Umar (RA) ya ce, ‘Na rantse da Wanda numfashin Ibn Umar ke hannunsa, da daya daga cikinku yana da misalin dutsen Uhudu na zinari, ya ciyar da shi ta hanyar daukaka addinin Allah, ba za a karba (masa) ba har sai ya yi imani da kaddara.” Sai Ibn Umar (RA) ya ba da dalili da fadar Annabi (SAW) cewa, “Rukunan imani su ne, yin imani da Allah da Mala’ikunsa da Littattafansa da Manzanninsa, da Ranar karshe, sannan kuma ka yi imani da kaddara ta alheri ko sharri duk daga Allah ne.” (Imam Muslim ya ruwaito).
An samu Hadisi daga Ubada dan Samit (RA) yana ce da dansa: ‘Ya dana! Ba za ka samu dandanon imani ba, sai ka san cewa duk abin da ya same ka da ma ba a kaddara zai kubuce maka ba, kuma abin da ya kubuce maka da ma ba a kaddara zai same ka ba. Domin na ji Annabi (SAW) yana cewa, “Farkon abin da Allah ya fara halitta shi ne alkalami. Sai Allah ya ce masa ‘rubuta!’ Sai alkalami ya ce, ‘me zan rubuta Ya Ubangiji?’ Sai Allah Ya ce, ‘ka rubuta duk ayyukan bayi har zuwa Ranar Tashin kiyama.” Sai Ubada (RA) ya ce, “Kuma ya dana! Na ji Annabi (SAW) ya ce ‘duk wanda ya mutu ba a kan wannan ba, to ba ya cikin al’ummar Annabi (SAW).”
Imam Ahmad ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Farkon abin da Allah Ya halitta shi ne alkalami. Sai Allah Ya ce ‘Rubuta ayyukan bayi har zuwa Ranar Tashin kiyama”. Shi ma dan Wahab ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Allah zai kona duk wanda bai yi imani da kaddara ba, na alheri da na sharri da wuta.”
Imamu Dailami ya ce, “Na zo wajen Ubayyu bin Ka’ab na ce zuciyata tana shakka a kan kaddara, amma ka yi min wa’azi ko Allah ya tafiyar min da wannan shakkar. Sai Ubayyu ya ce, “To wallahi ina fada maka da za ka ciyar da kwatankwancin dutsen Uhudu na zinari Allah ba zai karba ba, sai ka yi imani da kaddara.” Shi kuma imani da kaddara shi ne duk abin da ya same ka da ma ba a kaddara ya kubuce maka ba. Kuma abin da ya kubuce maka dama ba a kaddara ya same ka ba. To duk wanda ya mutu ba a kan wannan ba dan wuta ne!” Sai na bar Ubayyu bin Ka’ab na zo wajen Abdullahi bin Mas’ud da Huzaifatul-Yamani da Zaidu dan Sabit suma suka fada min daidai abin da Ubayyu ya fada min kuma dukkansu suka ce Annabi (SAW) ne ya fadi haka. (Imam Lakin ya ruwaito).
Bani na Sittin da daya: Masu yin hotuna:
An samu Hadisi daga Abu Huraira (RA), Annabi (SAW), ya ce, “Allah ya ce a Hadisin kudsi, “Babu wanda ya fi zalunci kamar wanda yake halitta irin Tawa. To su halicci kwaya mana ko kwayar zarra idan za su iya, ko su halicci sha’ir mana idan sun isa masu halitta.” (Bukhari da Muslim suka ruwaito).
An samu Hadisi daga A’isha (RA) cewa Annabi (SAW) ya ce, “Wadanda suka fi kowa tsananin azaba Ranar kiyama su ne wadanda ke sassaka gumaka su kamanta su da irin halitar Allah.” Ibn Abbas (RA) ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Duk wani mai yin mutum-mutumi dan wuta ne, kuma idan kiyama ta yi, za a sanya wa duk wani mutum-mutumi da ya yi rai su rika yi masa azaba a wutar Jahannama.” A wata ruwayar kuma Annabi (SAW) cewa ya yi, “Duk wanda ya yi mutum-mutumi a duniya za a tilasta masa ya hura wa wannan mutum-mutmin rai alhali kuma ba zai iya hura masa rai ba.”
Imam Muslim ya karbo daga Abu Huyyaj ya ce, Aliyu ya ce masa, ko kana so in aike ka da abin da Annabi (SAW) ya aike ni? Ya ce, kada ka bar wani hoto a bayan kasa har sai ka shafe shi, ko wani kabari wanda ya yi tudu sai ka daidaita shi ya yi daidai da sauran kaburbura.
Babi na Sittin da Biyu: Yawan rantsuwa:
Allah Ya ce, “Ku kiyaye rantsuwoyinku.” (Ma’idah: 89). An samu Hadisi daga Abu Huraira (RA), Annabi (SAW) yana cewa, “Rantsuwa a cikin ciniki tana taimakawa a sayar da abu da tsada, amma tana rage albarkar kudin.” (Bukhari da Muslim suka ruwaito).
An samu Hadisi daga Suleiman shi kuma daga Annabi (SAW) ya ce, “Mutum uku Allah ba zai yi magana da su ba, ba zai kuma tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai radadi. Su ne, tsoho mazinaci da talaka mai girman kai da wanda ya sanya rantsuwa da Allah garkuwa wajen saye da sayarwarsa.” (Imam dabrani ya ruwaito).
Imrana dan Hussain ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Fiyayun mutane su ne wadanda nake tare da su, sai wadanda ke bin su, sannan wadanda suka zo bayansu.” Sai dai Imran ya ce, na manta Annabi (SAW) bayan karninsa ya ce karni biyu ne ko uku? “Sannan wadansu mutane za su zo wadanda suna ganin abu amma ba za su ba da shaida ba, kuma za su rika ha’intar mutane, ba za su rike amana ba kuma za su rika yin alkawari amma ba za su cika ba, kuma kiba za ta rika bayyana a cikinsu (saboda rashin damuwarsu da rashin tsoron Allah balle su yi tunanin lahirarsu).” Ibn Mas’ud (RA) ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Fiyayyun mutane su ne na karnina, sai karnin da yake biye da wanda ke bin wannan, sannan da wanda yake bin sa. Sannan wadansu mutane za su zo wadanda rantsuwarsu za ta rigayi shaidarsu, ko shaidarsu ta rigayi rantsuwarsu.”
Ibrahim ya ce, tun muna yara ake dukanmu a kan in za mu yi shaida to mu fadi gaskiya, idan kuma muka yi alkawari, to mu cika.
Babi na Sittin da Uku: Cika alkawarin Allah da ManzonSa:
Allah Ya ce, “Ku cika alkawarin Allah idan kuka dauki alkawarin. Kada ku warware rantsuwoyinku bayan kun riga kun kulla su. (Ta yaya za ku warware alkawarinku alhali ga shi) hakika kun sanya Allah wakili a tsakaninku. Duk wanda ya aikata haka, to Allah Yana sane da abin da kuke aikatawa.” (Nahl: 91).
An samu Hadisi daga Buraida (RA) ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Idan Annabi (SAW) ya zabi shugaba a cikin runduna, to farkon abin da Annabi (SAW) yake yi masa wasiyya da wadanda suke tare da shi, shi ne a kan tsoron Allah.” Sai Annabi (SAW) ya ce musu, “Ku tafi yaki da sunan Allah domin daukaka addini. Ku yaki duk wanda ya ki yarda da Allah. Ku yi yaki amma kada ku yi shisshigi, kada ku yi yaudara, kuma kada ku yi mummunan kisa (wato kada a yanke hannu ko kafa ko kunne ko hanci sannan a kashe mutum) kuma kada ku kashe yara. Idan kuka hadu da mushrikai ba za ku fara yaki kai-tsaye ba sai kun kira su zuwa ga abubuwa uku. Kowane daya suka yarda daga ciki, to kada ku yi yakin. (Na farko) ku kira su zuwa ga Musulunci, idan suka amsa, ku karbi Musuluncinsu. Sannan ku kira su da su bar garuruwansu su dawo Madina, idan suka yarda da wannan kaurar to duk abin da za a bai wa muhajiri to su ma za a ba su kuma wani hukunci da yake kansu to yana kan muhajiri. Idan kuma suka ce su ba za su yi hijira ba, to suna iya zaunawa a gidajensu su zama kamar Larabawan kauye wadanda ba su fita yaki, kuma hukuncin Allah yana gudana a kansu, amma fa ba su da komai cikin ganima ko wani alheri da aka samu ba a yaki ba, sai idan sun yi yaki tare da Musulmi to za a ba su abin da ya kama a ba su. (Na biyu) Idan suka ki Musulunta, to, sai su ba da jizya (wato haraji). Idan suka yarda suka ba da jizya, to kada a yake su. (Na uku) idan suka ki ba da jizya, to sai ku nemi taimako daga wajen Allah ku yake su.
DSP Imam Ahmad Adam Kutubi, Zone 7 Police Headkuaters Wuse Zone 3, Abuja, 08036095723