✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tattaunawa ta musamman a kan littafin Alfu Laila Wa Laila (Dare Dubu Da daya)

Wannan tattaunawa mai muhimmanci, an gabatar da ita ne a shafin marubuta na ‘Mace Mutum’ da ke dandalin sadarwa na Facebook a cikin watan Oktoba…

Wannan tattaunawa mai muhimmanci, an gabatar da ita ne a shafin marubuta na ‘Mace Mutum’ da ke dandalin sadarwa na Facebook a cikin watan Oktoba na bana. Marubuta da masana ne suka tattauna game da al’amarin kamar haka:

Tun farko an fara tattaunawa ne a kan hasashen da ake yi na satar fasahar littafin ‘Kulu’ na Bala Anas Babinlata, da kamfanin shirya fina-finan kasar Hindu watau Bollywood suka yi. A cikin tattaunawar ne batun littafin ‘Alfu Laila Wa Laila’ ya sadado kuma ya sace shirin kacokan. Tattaunawar ta soma ne kamar haka, inda Kabiru Yusuf Anka ya bayyana cewa:
“Yadda Indiyawa suka saci fasahar Bala Anas: Labarin ya faro ne tun lokacin da aka fara ganin wani fim din Indiya. Take aka ga kwabo-da-kwabo fim din ya yi kama da littafin shahararren marubuci Bala Anas Babinlata, wato ‘Kulu.’ Makaranta da masu nazari suna matukar girmama fasahar Bala. Ba sa yarda cewa Balan shi ya saci fasahar, koda sun kkara kallon fim din, ciki har da ni.
Da haka ta faru sai tunani ya zo wa masu kokarin kare Bala cewar a je a duba shekarun da aka buga littafin da kuma yin fim din. Cikin ikon Allah da aka duba sai aka ga an buga littafin da kusan shekaru biyar sannan aka fara aikin fim din, aka sake shi. To a nan kuma sai aka fara tunanin yaya ke nan? Saboda rashin adalci sai kuma ake tunanin ai kawai arashi ne, labari ya zo daya. Ka ji fa, da a ce an tarar da cewa fim din ya riga littafin; da shi ke nan sai a ce Bala ya saci fasahar Indiya.
To bari ku ji yadda aka tabbatar satar fasahar Balan suka yi.
Wasu shekaru da suka wuce, fina-finan Hausa sun yi gagarumar karbuwar da suka disashe fina-finan Indiya a Duniyar Hausawa. A lokacin ’yan fim sun fara rungumar labarai daga marubuta. Faruwar hakan ya sa hankalin dillalan fina-finan Indiya na can da na nan tashi, don za su rasa abincinsu. Sun fara ne da bincikar yadda hakan ta faru. A cikin binciken nasu sun gano cewar daya daga cikin dalili shi ne labarai da fina-finan Hausar suka samu kuma labaran daga yawanci marubuta littattafan Hausa, sai kuma suka fara bincike a kan ire-iren labaran Hausawan. Sun kwashi littattafai da yawa na Hausa sun yi nazarinsu, a ciki aka samu abin da muke da tabbaci kamar haka: Labarin littafin ba gama gari ba ne. Idan labarin Balan yana samuwa kuwa to ’yan siddabarun da ya yi amfani da su a littafin akwai su a fim din.
Bayan wannan, kowa ya yarda duk duniya Indiya barayin fasaha ne. India suna yawan yin fina-finai, don haka labarai sun yi masu kadan. Hakan ya sa suke rarumen labarai daga ko’ina ko su yi maimaici a fina-finansu. (Zan kawo sunan fim din don a kuma tabbatarwa).
Sannan, zan yi magana a kan yadda kullum marubucin Hausa ke mayar da kansa baya ta fuskar satar fasaha, alhalin yana da fasahar kuma akwai hanyoyi da dama da ake ganin fasahar har a iya sacewa.”
Da Kabir Anka ya diga aya sai kuma Bukar Mada ya bullo da nasa bayanin, kamar haka:
“Na yarda da wannan bayani naka Anka, dari bisa dari. Indiyawa barayin labari ne na karshe, sai dai abin takaici mutanenmu ba su yarda da haka ba. Kodayaushe labarin Hausa ya zo daidai da na Indiya sai su dauka na Indiya din ne aka sata.
Akwai wata hikaya ta ‘Ali Baba Da barayi Arba’in’ da na fassara daga littafin ‘Arabian Nights,’ wanda shi ma Turawa ne suka fassara shi daga ‘Alfu Laila Wa Laila.’ Ina buga labarin a shafin ‘Waziri Aku.’
Da yawa daga cikin masu sharhi, cewa suka yi fim din Indiya ne na fassara, wanda ni ban ma san da akwai wani fim da ya kwaikwayi wannan labari ba. Abin da masu sharhin ba su sani ba shi ne, tun kafin a san da wata abu wai ita kyamara, littafin ‘Alfulaila Wa Laila’ yake, ballantana a ce labarin fim din ne aka sa a littafin.”
Bayan Bukar Mada ya kawo gaci, sai Fatuhu Mustapha ya amshi batun, inda ya bayyana cewa: “Bukar Mada, littafin ‘Alfu Laila’ asali littafin Indiya ne, kodayake da Larabci aka rubuta shi. In ka lura, za ka ga duk sunayen mafi akasari na Indiyawa ne, irinsu Sharazzad, Aliyu Nuradden, Anisil Jalisi da sauransu. Zan kawo maka tarihin littafin da bayanai da masana suka yi a kansa in kana so.”
Nan take Bukar Mada ya dawo da ta’aliki game da bayanin Fatuhu, inda ya ce: “Alfu Laylah Wa Layla’ littafin labarai ne na mutanen Asiya da Gabas ta Tsakiya, ba na Indiyawa ne ba kadai. An rubuta shi tun farko a kasar Parisa, watau Iran. sunansa na asali Hazar Afsanah, daga baya ya koma a Larabce.”
Zaren takaddamar ya ci gaba, a yayin da Fatuhu Mustapha ya ce: “Gaskiya ne, labarun Farisawa ne, ba na Indiyawa ba. Kodayake an hakikance rayuwar Indiyawa ta fi tasiri a cikin littafin, musamman ‘Kama Sutra’ da kuma labarun ‘Tutuname.’ Ina ganin shaharar da Radhiya Sultan ta yi da kuma tasirin mulkinta a Farisa ya sanya Farisawa suka fi maida himma ga rayuwar badala ta Indiyanci.
Ya kamata a lura, kafin Ba’indiye ya saci fasaha a wurin Bature, Bature ne ya fara satar masa fasaha. Sinimar Indiyawa ta fi ta Turai da ta Girka dadewa. Sai dai nasarar da Turawa suka yi, musamman a bangaren kimiyya da fasaha, ita ta sa ake zaton Indiyawa sun saci fasahar Turawa.”
Shi kuwa Ado Abubakar Bala, ga abin da yake cewa: “Fatuhu Mustapha, ban yarda ba. Sinimar Girkawa ta fi ta kowa dadewa a duniya, Sophocles ya rubuta wasan kwaikwayon ‘Oedipus the King’ tun a 429 K.I. (Kafin Isa). Wadannan shekarun tun kafin haihuwar Annabi Isa (AS) ke nan.”
Ita kuwa Bilkis Abdul Ingawa, tambaya ta yi cewa: “Tambayata ga malamai, wa ya rubuta ‘Alfu Laila Wa Laila?’ Ina yawan jin sunan littafin.”
Nan da nan Bukar Mada ya amsa da cewa: “Ki duba wannan ‘zaren’, duk bayanan da kike bukata a kan littafin za ki samu, sai dai Turanci ne: http://en.wikipedia.org/wiki/One_Thousand_and_One_Nights
Daga nan ne sai ita Bilkis Bilkees Abdul Ingawa ta dawo, tana cewa: “Ikon Allah, wato ‘Ali Baba and the Fourty Thiebes’ ma duk a ciki yake, ban taba sani ba sai yau. A yadda na fahimta labarai ne daban aka tattara su wuri daya ya fito a matsayin littafi daya.”
Fatuhu Mustapha ya dora da cewa: “Bilkis, labari daya ne, kawai ’ya’ya aka yi masa, aka ba da labarin a darare 1001. Sharazzad ce ta ba da labarun, domin ta ceci ran ’yar uwarta. Farfesa Dabid Hofstard, wato Malam Mamman Kano, wanda daga baya ake kira Dauda dankano, shi ya fassara shi zuwa Hausa.”
Za mu ci gaba