✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tattalin arzikin Najeriya na raguwa – Masana

A ranar Talatar da ta gabata ce Kwamitin Tsara Harkokin Kudi na Babban Bankin Najeriya (CBN), ya kammala taron wuni biyu, inda ya yi gargadin…

A ranar Talatar da ta gabata ce Kwamitin Tsara Harkokin Kudi na Babban Bankin Najeriya (CBN), ya kammala taron wuni biyu, inda ya yi gargadin cewa tattalin arzikin Najeriya yana iya sake haduwa da masassara, muddin ba a dauki wasu matakai na daidaita al’amuran da suka wajaba ba.

Kwamitin ya ce babbar matsalar da ake fuskanta a yanzu ita ce ta rashin ci gaba wadda take rura wutar hauhawar farashin kayayyaki da kuma ja bayan da asusun ajiyar kasashen waje ke yi a kullum, sakamakon samun canji kan kudaden da suke shigowa. Kwamitin ya sha alwashin ci gaba da tafiyar da duk tsare-tsaren da yake yi don kauce wa hakan.

Ya ce za a ci gaba da tafiyar da ruwan bashi a kan kashi 14 cikin 100 yayin da aka bar ruwan kudin ajiya a kashi 22.5, sai kuma kudin ruwa na musamman a kashi 30, yayin da zauren MPR zai ci gaba da lura da irin kudin ruwan da bankuna suke amsa, sai kuma CRR kan kudin da ake ajiyewa da aka amince wa bankuna daga nan za su rika harkokin bada bashi da suke yi.

Bugu da kari kawamitin ya cewa matakin da ya dauka na ci gaba da tsaurara tsare-tsaren tattalin arziki, zai sa wa hauhawar farashin kayayyaki tarnaki. Wannan kuma shi ne zai bunkasa karuwar shigowar kudade, kuma ya daukaka matsayin asusun ajiyar kudaden waje, sannan bangaren sayen hannun jari ya kara bunkasa.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya bayyana cewa kwamitin ya lura da yadda tabarbarewar tattalin arziki ke kara tasowa, inda  kudaden da ke  hannun al’umma ke gaza wadatarsu biyan bukatu, duk da cewa Naira tana kara samun karfi.

Gwamnan ya nanata cewa bayan taron da suka gabatar cikin watan Yuli saboda sake dubawa da nazarin bangaren tattalin arziki, da farko an duba yadda rumbun ajiya na waje ya samu karuwa sosai, sai kuma ya yi kasa da kuma yadda bayan magance masassarar tabarbarewar tattalin arziki wata 18 da suka shude, amma yanzu abin yana neman dawowa.

“Duk da yake an taba shiga  mawuyacin halin tabarbarewar tattalin arziki musamman ma ruwan da yake tattare da bashi. Dalilin da ya sa muka ci gaba da tafiyar da tsare-tsaren tattalin arziki a karo na 11,” inji shi.

Don haka babban bankin ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya cewa ta kawo dauki wajen daukar wasu matakai, musamman ga masana’antun da tuni suka durkushe. har zuwa yanzu dai Najeriya tana ci gaba da tafiya ne da kashi 12.