Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam), tare da alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi sawunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.
Bayan haka, yau, 27 ga Zul-kida shekara ta 1436 Bayan Hijira, insha Allah a takaice, za mu dubi rantsuwar da Allah Ya yi da kwanaki goma na watan Zul-Hajji, sannan sai bayani kan sha’anin Layya da Sallar Idi da fatan Allah Ya sa bayanin ya amfane mu duniya da Lahira.
Wadannan kwanuka goma na watan Zul-Hajji, su ne wadanda Allah Ya yi rantsuwa da su, kamar yadda malamai (kamar su ++Abdullahi Ibn Abbas da Ibn Zubayr da Mujahid da wasunsu cikin Salaf da wadanda suka maye gurabunsu) suka bayyana, yayin da Allah Ya ce, “Ina rantsuwa… da Darare Goma… Ko a cikin wadannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)?” Surar Fajr, aya ta 1- 5.
Abdullahi dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Babu wasu kwanuka da aikin alheri ya fi soyuwa a cikinsu (a wajen Allah), kamar wadannan kwanuka (yana nufin kwanukan goman farko na watan Zul-Hajji).” Sai (sahabbai) suka ce, “Ya Manzon Allah, ko da jihadi don daukaka Kalmar Allah?” Ya ce, “Ko da jihadi cikin daukaka Kalmar Allah, sai dai (a ce misali) in mutum ya fita da ransa da dukiyarsa, kuma ya kasance bai dawo da komai daga ciki ba (wato ya yi shahada kuma dukiya ta kare).” Buhari ne ya ruwaito wannan Hadisi.
Imam Abu Zakariyya Yahya bn Sharaf Annawawiy, a cikin littafinsa Riyadhus Salihin (Babi na 226, shafi na 321, Hadisi na 1,257) ya gabatar da wata manuniya kan falalar yin azumi da waninsa a cikin wadannan kwanaki goma, inda ya gabatar da wannan Hadisi.
Lallai yin azumi yana daga cikin mafi girman ayyukan alheri, saboda ba a san iyakar ladarsa ba, don Allah ne Ya ce Shi Zai biya ladarsa, kamar yadda Imam Buhari da Imam Muslim suka ruwaito daga Hadisin Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), daga Ma’aikin Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). A cikin Hadisin, Allah Ya ce, “…saboda shi (azumi) Nawa ne, Ni ne Zan sakamka shi (Zan ba da sakamakonsa)….”
Saboda haka wannan abin kwadayi ne da ya kamata a ja hankalin ’yan uwa su yi kokarin yin azumin, matukar suna iyawa a cikin wadannan kwanuka goma saboda Allah, don su samu lada mai gwabi, wato bayan karin kokari wajen yawaitawa da kuma kyautata sauran ayyukan ibada, domin fin soyuwarsu wajen Allah Ta’ala.
Bugu da kari, Abu Sa’idunil Khudriy (Allah Ya yarda da shi), ya ce, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Babu wani daga cikin bayin Allah da zai azumci wata rana saboda Allah kawai, face Allah Ya nisantar da fuskarsa daga wuta, nisan kharifa saba’in.” Imam Buhari da Imam Muslim suka ruwaito wannan Hadisi. Abin da ake ce ma kharifa, kamar yadda aka bayar da ma’anarsa, shi ne tsawon tafiyar mil guda.
Da yake azumtar wadannan kwanuka mustahabbi ne ba dole ba, wanda ba zai iya yin su duka ba, to ya dage ya azumci ranar Arafa, wato ranar 9 ga watan saboda falalarsa. Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam), lokacin da aka tambaye shi game da azumtar ranar Arafa ya ce, “Yana kankare (zunuban) shekarar da ta wuce da na wacce ake ciki.” Wato shekara biyu ke nan! Imam Muslim ne ya ruwaito shi daga Abu kattadah (Allah Ya yarda da shi).
Wadannan kwanaki goma za su fara ne daga ranar Litinin, in an ga wata ko Talata, in Zul-kida ya cika, in Allah Ya so. Allah Ya ba mu dacewa da alheran da ke cikinsu, Ya kare mu daga dukkan sharri, amin.
Sai batun Layya: Layya tana cikin mafi girman ayyuka kyawawa a cikin wannan wata na Zul-Hajji, kuma Sunnah ce mai karfi a addinin Musulunci. Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Babu wani aiki, daga cikin ayyukan alherin da dan Adam (Musulmi) zai aikata a Ranar Sallah, wanda ya fi soyuwa a wajen Allah, kamar zubar da jini (yin Layya), saboda haka ku dadada zukata da shi.” Imam Tirmizi da Ibnu Majah da Haakim suka fitar da Hadisin daga A’isha (Allah Ya yarda da ita).
Allah Ya ce, “Kuma ka (tsayar da) Sallah saboda Ubangijinka, kuma ka yi suka (wato Layya da hadaya)…” Surar Alkausar aya ta 2.
Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) ya ce “Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance yana Layya da rago biyu kosassu, masu maiko, masu (manyan) kahonni. Sai ya yi basmala (fadin Bismillahi), ya yi kabbara (fadin Allahu Akbar), ya dora kafarsa a gefen wuyan (abin yanka) ya yanka. Ya yi yankan da kansa.” Buhari da Muslim suka ruwaito shi.
Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Wanda duk yake da wadata kuma bai yi Layya ba, to kada ya kusanci masallacinmu (wato ya yi zamansa a gida kawai).” Imam Ahmad da Ibnu Majah suka ruwaito shi, kuma Imam Hakim ya inganta shi. Wasunsu, masu fitar da Hadisi sun rinjayar da wakafin (tsayar da) Hadisin ga Abu Huraira. Wadanda suka danganta Hadisin ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) tabbatattu ne (wato sikat ), a fagen amincinsu kan haka.
Imam Darakudniy da Hakim sun fitar da Hadisi daga Abdullahi dan Abbas (Allah Ya yarda da shi), cewa Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Abu uku a kaina farilla ne, amma a kanku tadawwi’i. Wadannan abubuwa kuwa su ne: suka (Layya); yin Sallar Wutiri da yin raka’o’in Alfijir.”
Wannan ya nuna karfin Sunnar Layya, hasali ma malamai (irin su) Rabi’ah da Al’auza’iy da Abu Hanifa da Allaisu da wani yanki daga masu bin Mazhabar Malikiyya suna ganin wajiba ce ga wanda yake da iko. Sai dai jamhurun malamai, wadanda suka hada da Imam Malik da Shafi’i da Ahmad da Is’hak da Abu Sauwr da Almuzanniy da Ibn Munzir da Dawud da Ibn Hazam da wasunsu, sun tafi a kan cewa Sunnah ce, ba wajiba ba.
Nau’in dabbobin Layya: Ana farawa da rago lafiyayye; sannan sai tunkiya; sai bunsuru lafiyayye; sai akuya; sai sa da saniya; sai rakumi da taguwa. Amma a hadaya a Makka, ana farawa daga rakumi zuwa akuya. Al’ada ce a ki ko a ji kunyar yin Layya da bunsuru ko akuya.
A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce, “Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya umurci a kawo rago mai kahonni, wanda ya taka baki (a kafafunsa); ya kwanta a kan baki (a cikinsa); kuma ya yi dubi a cikin baki (a idanunsa), sai aka zo da shi (don yin Layya), sai ya ce, “Ya A’isha! Kawo min wuka, ki wasa ta da dutse.” Sai na aikata haka (inji A’isha), sai ya karba, ya kama ragon ya kwantar da shi, sannan ya yanka, bayan ya ambaci sunan Allah, ya yi addu’a: “Ya Allah, Ka karba daga Muhammad da alayen Muhammad da kuma al’ummar Muhammad.” Imam Muslim ne ya ruwaito shi. A wata ruwayar kuma ya ce, “Bismillahi wallahu akbar.”
Lallai ne kowace dabbar Layya ta kasance lafiyayya, wadda ba ta da kowace bayyanannar nakasa.
Za mu dakata a nan sai mako na gaba.
Wassalamu alaikum warahmatullah!
Tasirin Darare Goma na Zul-Hajji da bayanin Layya da Sallar Idi
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin…