✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tasirin Abinci Ga Ingancin Ibadar Aure

Assalamu Alaikum, marhabin da sake haduwarmu cikin wannan fili. Ga bayani kan tasirin abincin da ma’auarata suke ci, ga inganta ko raunana lafiyar ma’aikatar sha’awarsu;…

Assalamu Alaikum, marhabin da sake haduwarmu cikin wannan fili. Ga bayani kan tasirin abincin da ma’auarata suke ci, ga inganta ko raunana lafiyar ma’aikatar sha’awarsu; da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.

Masarrafin Sha’awa: Shi ne abinci! Abincin da muke ci na taka muhimmiyar rawa wajen inganta ko nakasa sha’awar dan’adam. Yanayin rayuwarmu ya sa duk abincin da aka samu sakawa ake a ciki, hatta wadanda suka san illolin wasu abincin, sai kawai su kau da kai su ci abincin da suka san yana da illa ga lafiyar sha’awarsu da jikinsu don dadinsa ko don nauyin bukatarsu a lokacin. Yana da kyau dan’adam a koda yaushe ya kasance mai kiyayewa da kula da irin abin da zai kai cikin bakinsa, domin ba dadinsa a baki ne kadai ba, amfani ko illar da zai yi yayin da aka sarrafa shi ya shiga cikin jini shi ne babban abin la’akari. Yawanci kayan dadin wannan zamanin, wadanda ake ganin cin su gayu ne da wayewa ba abin da suke haifarwa ga sha’awar dan’adam sai nakasu haka kuma ga lafiyar jiki gaba daya.
Kowane kalar abinci akwai wani bangare na ibadar auren da zai habaka, wani zai sanya nishadi da jin dadi cikin zuciya da ma’aikatar hankali, wani na taimakawa wajen malalar jini cikin jijiyoyin ibadar auren, wani kuma kara yawan sinadaran sha’awa cikin jini ko inganta masarrafar da ke sarrafa su cikin jiki. Motsuwar sha’awa, jin dandanonta da cimma biyan bukatar sha’awa ba su tabbata sai an samu abubuwan nan guda uku suna aiki dai-dai da dai-dai:
1. Ya kasance akwai wadatar sinadaran sha’awa a cikin jini.
2. Ya kasance jini na malala da gudana sosai a cikin jiki.
3. Sannan kuma ya kasance zuciya; ruhi da ma’aikatar hankalin mutum suna cikin nishadi da wadatar zuci.
Duk idan daya daga cikinsu ya sami nakasu, to ibadar aure za ta zama mai rauni ko ma ta ki yuwuwa gaba daya. Su kuma abubuwan nan guda uku da na zana ba sa tabbata sai da cikakkiyar lafiyar jiki, shi ya sa duk wani abinci mai inganta lafiyar jiki to tabbas zai inganta lafiyar sha’awa kuma, domin dai gaba daya sassan jikin dan’adam na aikin taimake ni-in-taimake ka ne, duk abin da ya shafi wani bangare na jiki zai yi tasiri ga kusan duk ilahirin jiki. Don haka mu gane cewa cin abinci mai kara lafiya shi ne wayewa ba cin abincin gaye-gaye, irin na zamani ba. Abubuwan kara lafiya kuwa ba kamar irin ganyayyaki, kayan marmari da ‘ya’yan itatuwa. Akwai mamakin yadda wasu ‘yan gayun Hausawa suke ganin cin ire-iren ganyayyakinmu na gargajiya, kamar su zogale a matsayin kauyanci, su kuwa Turawa, asalin gayun, suna kashe kudi masu yawa wajen kai su kasashensu suna amfani da su don sun san darajarsu wajen inganta lafiyar jiki da kiyaye jiki daga kamuwa da cututtuka. Cin kala-kalar ganyayyaki da ‘ya’yan itatuwa da ‘yan kauye suke yawan yi yana daga cikin abin da ya sa suka fi na birni lafiya mai armashi, kuma shi ya sa da wuya ka ga mutumin kauye da katon ciki kamar an kifa tukunya, duk kayan dadin nan da dan birni yake ci su ne suke sa masa wannan katon ciki, wasunmu suna ganin katon cikin nan albarka ce, ya za a yi abin da ya canza maka siffarka ta asali ya taba zama albarka? Sayyidina Umar (RA) ya kirayi irin wannan cikin da “Mafi bala’in ciki”. Ina kira ga ma’aurata da su guji yawancin magungunan karin sha’awa na zamanin nan, domin komai dadin da aka ji wajen amfani da su, illar da suke haifarwa daga baya tana sa a ji dama ba a yi amfani da su ba. Yawancinsu kuma suna dauke da gurbatattun sinadaran nan na carcinogens, masu sa cutar daji ko sankara (cancer).
1.Kalar Abincin Da ke Nakasa Ma’aikatar Sha’awa
•Abinci masu illa ga sha’awar dan’adam sun hada da duk wani abinci mai dauke da sinadarin caffein irin su Nescafe da shayi da goro da lemon kwalba(coke, pepsi) da sauransu. Domin wannan sinadarin yana rage sarrafa sinadarin cortisol wanda yake da nasaba wajen habaka aikin sinadaran sha’awa da kuzarin jiki.
•Sai abinci masu dauke da sinadarin cholesterol, irin su duk wani soyayyen abinci, jan nama, abincin kamfani, abincin gwangwani da sauransu. Shi wannan sinadari akan ajiye shi ne a matsayin kitse a hanyoyin jini, wanda yakan rage karfin gudanar jini har a jijiyoyin al’aura, wanda sai jinin ya malala cikinsu ne kafin sha’awa ta hauhawa.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.