✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tashin hankali illa ce ga kasa

Inna lillahi wa’inna ilahi raji’una !  Na fara ambatar wannan kalmar ne abisa da fiyayyen halitta Annabin rahama na cewa duk abin da ya tsoratar…

Inna lillahi wa’inna ilahi raji’una ! 

Na fara ambatar wannan kalmar ne abisa da fiyayyen halitta Annabin rahama na cewa duk abin da ya tsoratar da ku ko kuma Annoba ta afka mu ku, to ku kira wannan kalmar mai girma waton Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’una ! Na kuma ambaci Kalmar ne ganin karatowar watan biyu na sabuwar shekara da muke ciki, don gudun zubar jini da hasarar dukiyoyi ita ma na amba ce ta ne a matsayina na dan Adam kamar kowa. Domin ni dai ban san abin da gobe za a yi ba, to amma duk wanda ya sanya tabaraunasa na hasashen zabukan nahiyar Afrika, musamman ma a Najeriya da hayakin siyasa ke kara turnuke kasar .
Ni dai wannan hasashen nawa kwata-kwata ba na fatar ya faru a Najeriya.Domin ni ba ni da wata kasa da tafi Najeriya, fatana dai ayi zabe lafiya a kuma a gama lafiya, tare da shugabanni nagari da bunkasar tattalin arzki mai amfani ga talakawan Najeriya. Tun shigowar mulkin dimokuradiyya a Najeriya duk lokacin da kakar zabe ta zo, to fa sai an samu hasarar rayuka da dukiyoyi a
Najeriya, musamman ma a Arewa. Saboda haka don Allah ga tambayata ga ‘yan Najeriya da malaman siyasa shin, wai iya siyasar ne ba mu yi ba ne? ko kuma dacewa ne siyasar ba ta yi da ‘yan Najeriya ba? Sannan ko kashe-kashe da lalata dukiyoyi a lokacin yakin neman zabe da ma bayan zabe suna faruwa a kudancin Najeriya? Sannan mene ne ya sanya matasan mu suka kasa bambance tulin hanjin jimina da na zakara wajen watsi da ‘yan gumamar siyasa masu ingaza su da ayyukan tarzoma a lokacin zabe da ma bayan zabe? Sannan mene ne ya sanya mutanen Kudu da na Arewa ke ci gaba da gudun hijira zuwa yankunansu domin kauce wa tarzomar bayan zabe?
Don haka ya kamata iyaye da malaman addini da shugabannin jama’a su yi abin da ya dace wajen jan hankalin jama’a akan illolin da ke tartare da tashin hankali. Domin shi tashin hankali bai taba gina kasa ba. Haka ma ya kamata ‘yan siyasa da su taka wa magoya bayansu birki daga tashin hankali.Domin zaman lafiya ya fi zama dan sarki . Yin zabe da rashinsa a Nijeriya duk matsala ce ga zaman lafiyar kasa. Don haka a ma a yi zaben a huta. Sai dai ya kyautu tun daga Gwamana har shugaban kasa da su sauka a bada rikon kwarya domin gudanar da zaben gaskiya da adalci. Domin fa idan a haka ne za a gudanar da zabe a Najeriya to fa ko shekara 60 aka yi ba za a taba samun zaben gaskiya ba. Haka ma kashe-kashen ba za su taba sauki ba.
Sani na ga Ubangijin Musa Da Isah. To amma masu iya magana na cewa alamar icce mai ‘ya’ya daga furensa ake gane shi, fatana Musulmi da Kiristan Nijeriya su hade kansu tare da yi wa Nijeriya addu’a. Abu na kusa da na karshe shi ne Hukumar zaben Najeriya da ta kwana da sanin cewa makullan kasa na hannunta, waton makullan zaman lafiya da akasin haka. Da fatan za a gudanar da karbabben zabe ga kowa da kowa, ba tare da sanya amaja ba.
Lissafina na kara dagulewa akan sha’annin siyasar kasata. Haka zalika ya kyautu jami’an tsaron Najeriya da su yi abin da ya dace wajen watsa wa tarzomar bayan zabe ruwa, duk da cewa tarin dokokin da Najeriya ke tunkaho da su ba sa aiki akan masu laifuffuka duk da cewa jami’an tsaro na kukan cewa ba su da kayan aiki, uwa uba suna cewa ‘yan siyasa na yi musu karan tsaye ga aikinsu.
Ina kara rokon Allah duk mai hannu ga zubar da jinin jama’a a ko’ina yake a Najeriya ko kuma a kowacce jam’iyya yake Allah ya tona asirinsa, tare da annobar karyar tattalin arzikinsa da gushewar hankalinsa.

Hassan Muhammad Binanchi,Daga Unguwar Magajin Garin Sakkwato/[email protected]/08062445805