✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tashe-tashen hankula a kasar nan

A kwanakin baya mun ga abubuwa iri-iri a Najeriya, wasu na ban haushi, wasu na ban ala’ajabi. Wani abin in an yi sai ka ga…


A kwanakin baya mun ga abubuwa iri-iri a Najeriya, wasu na ban haushi, wasu na ban ala’ajabi. Wani abin in an yi sai ka ga kamar an raina talaka. Alal misali kimanin mako biyu da suka wuce ne wadansu ’ya’yan Jam’iyyar PDP suka canja sheka zuwa Jam’iyyar APC a Jihar Katsina.  A wajen dan siyasar Najeriya musamman wanda ya mayar da siyasa saye da sayarwa,  wannan ba wani abu ba ne don dan siyasa ya tashi daga wata jam’iyya zuwa wata jam’iyyar.

Hakazalika a makon ne, aka kashe kasurgumin dan ta’addan nan, maridi wanda ya kashe dimbin mutane a Jihar Zamfara wato Buharin Daji. An dai kai gawarsa a wulakance zuwa Gusau babban birnin Jihar Zamfara inda kowa ke murna, ciki da wajen jihar. Fatanmu dai shi ne Allah Ya sa wannan shi ne karshen Buharin Daji. Ba mu fatan ko a mafarki mu kara samun Buharin Daji. Allah Ya sa kisan Buharin Daji ya zama shi ne sanadiyar kawo karshen ta’addancin gungun barayi, ’yan fashi da masu garkuwa da mutane a yankin.

Wani abin da ya ja hankali shi ne rikicin Benuwai da Taraba da Kudancin Kaduna da Jihar Filato. Kodayake yankin tsakiyar Najeriya inda ake kira da “Middle Belt” ba bako ba ne a harkar zubar da jinin jama’a, amma yana da kyau mu yi tambaya wai shin me ya sa rikicin addini da kabilanci a yankin tsakiyar Najeriya ya ki ci ya ki cinyewa?

Na san ko mai karatu za ka iya ba da wasu amsoshi. Babbar amsa ita ce,  rashin hukunta masu laifi. Me ya sa to ba a hukunta masu laifin? Wannan tambayar ma na bukatar amsa. Shi dai rikici irin wannan mafi yawanci kulla shi ake. Kuma mutanen da ke kulla rikici irin wannan akasarinsu shugabanni ne. Misali rikicin Zangon Kataf, wadanda suka tsara shi, suka ba da umarni aka aiwatar, manyan shugabanni ne, kuma kowa ya ga rahoton da kwamitoci da dama suka bayar, to amma babu wanda aka hukunta, sai aka koma ana bugun taiki, aka bar jaki.

Mu koma Jihar Taraba, rikicin Jukunawa da Tibi da aka sha fama da shi. Ina suka samu makamai? Wa ya ba su makaman su kashe junansu? Mutanen da ke harkar neman arziki ta hanyar noma da kasuwanci da aikin gwamnati, me ya kai su ga sayen makamai domin fada? Mutumen da ke zaune cikin daji, ina ya san wurin da zai sayo bindiga kirar AK 47? Kuma wace riba zai samu idan ya sayi bindiga tun da ba fashi da makami yake yi ba?

Wannan zai nuna maka duk akwai manyan attajirai da ’yan siyasa wadanda ke assasa wadannan rikice-rikice inda suke zuga talakawansu suna yi musu hudubar Shaidan a kan makwabtansu, suna amfani da jahilicinsu wajen fada musu karya da gaskiya game da makwabtansu, bayan sun yi musu hudubar karya sai su ba su bindigogi su je su far wa makwabtansu su yi ta kashe su. Daga karshe bayan sun kammala ta’asarsu, za ka ga koda wadanda jami’an tsaro za su kamo kananan ne, amma ba za a kama wadanda suka ba su horo da bindigogi da yunifom da kudi su je su aikata ta’addancin ba. Kuma kananan makasan da aka kama za ka samu su wadanda suka zuga su su yi ta’addancin sun bi ta bayan fage sun karbo su daga hannun jami’an tsaro.

Yanzu maganar da ake baki dayan yankunan Middle-Belt dauke suke da kungiyoyin daba da kisa (militia).  Ka dauki wani bangare a Jihar Adamawa inda kabilar bachama ke da kungiyar matasa makasa wadanda ake amfani da su a lokacin rikicin addini ko kabilanci. Mun ga irin ta’addancin da wannan kungiyar makasa ta ’yan kabilar bachama suka aikata wa Hausawa da Fulani a rikicin kwanan nan, inda suka yi kisan wulakanci ciki har da kashe jarirai da mata masu juna biyu.

A Jihar Taraba mai kabilu da yawa  kusan babu wata kabila in ka cire Hausawa da ba su da kungiyar matasa masu dauke da makamai. Idan kana so ka tabbatar da maganar da nake ba shaci-fadi ba ce,   ka bari sai rikicin kabilanci ya barke a Wukari ko Takum ko Mamabila ka ga ko karya nake yi.

A Jihar Filato wacce ake ganin ita ce hedkwatar fitina da sunan addini, kusan kowace kabila ta kafa daularta da sojojinta matasa wadanda ake amfani da su wajen kare muradun kabila ko addini. Yadda rikicin Jos ya faru inda har babbar Kasuwar Terminus aka kona, abin ya ba jami’an tsaro mamaki ganin yadda wadansu suka tara dimbin makamai ba tare da saninsu ba. 

kungiyar bata-gari da gwamnatin Benuwai ta kafa ita ce, ta farko da kai-tsaye ba tare da wata kwana-kwana ba da shugabanni masu assasa zubar da jini suka yi a Najeriya.

Gwamnan Jihar Benuwai ya yi abin da duk dan rajin kafa yankin Middle-Belt zai yi alfahari da shi. Lallai kuwa Samuel Ortom ya samu yabo da goyon bayan ’yan kabilarsa da wadanda ba ’yan kabilarsa ba amma suna da ra’ayin Middle Belt kamar ’yan jaridar Kudancin Najeriya da ’yan bokonsu. Samuel ya kafa kungiya, ya kuma  tsaga masu albashi da ba su makamai irin na zamani da yunifom. Duk wannan ya yi amfani da dokar da ya kafa ta hana yin kiwo ne. Yanzu wadannan ’yan banga da Ortom ya kafa, ba kawai ga hana kiwo za su tsaya ba, za a iya amfani da su a yaki wata kabila ko mabiya wani addini da sauransu.

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, Babban Sakataren kungiyar Muryar Talaka ta kasa  08165270879