✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tashar tsandauri ta Kano za ta lakume Dala miliyan 27 kafin ta fara aiki

Tashar zata fara aiki gadan-gadan nan da karshen shekarar 2022 za kuma ta samar da ayyukan yi kimanin 20,000.

Manajan Daraktan tashar tsandauri ta Dala dake Kano, Alhaji Ahmed Rabi’u, ya ce aikin samar da tashar zai lunkume zunzurutun kudi kimanin Dalar Amurka miliyan 27 kafin ta fara aiki.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake zagayen duba yadda aikin ke gudana a unguwar Zawaciki dake Karamar hukumar Kumbotso a jihar ta Kano, inda ya ce kashin farko na aikin za a kammala shi nan da 17 ga watan Yunin 2021 kan kudi Dala miliyan 17.

Manajan Daraktan ya kara da cewa tuni Gwamnatin Jihar ta ware kudi Naira biliyan 2.3 domin aikin gina hanyoyi da kuma katangar da zata kewaye tashar da kuma samar da wutar lantarki a wurin.

Rabi’u ya ce, “Muna son kammala aikin don kara samun kudaden haraji a aljihun gwamnati da rage yawan batan kwantenoni yiyin jigila daga Legas zuwa Kano.

“Da zarar mun kammala, kudin sufurinn kaya zai ragu sosai saboda yanzu haka kimanin miliyan N1.2 ake caji don dauko kwantena daga Legas zuwa Kano ta kan titi, amma ta jirgin kasa ba za a ringa karbar sama da N200,000 ba.

“Kwantenonin da aka sauke su a tashar ruwa ta Legas za a dauko su kai-tsaye ta tsohuwar hanyar jirgin kasa zuwa Kano cikin sa’o’i 24, sannan kuma aikin zai kara farfado da harkokin kasuwancin kasashen Sahara,’’ In ji shi.

Rabi’u, ya kara da cewa, wurin da ake gudanar da aikin ya kai kimanin fadin kadada 200 na kasar noma, kuma an ware shi ne don ya zama wata matattara ta inganta tattalin arziki.

Ana sa ran kammala aikin nan da watan Disamban 2021, kuma ana sa ran tashar ta tsandaurin za ta dauki Kwantenoni akalla 30,000.

Rabiu, yace tashar zata fara aiki gadan-gadan nan da karshen shekarar 2022 za kuma ta samar da aikin yi kimanin 20,000.