Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa tashar jiragen ruwa ta kan tudu za ta fara aiki a birnin Maiduguri nan da watanni shida ma su zuwa.
Zulum ya bayyana hakan ne a Jihar Legas a zantawarsa da manema labarai yayin ziyarar da ya kai wa Babban Sakataren Hukumar Kula da Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), Pius Akutah.
Gwamnan ya bayyana kwarin gwiwar cewa kafa hukumar NSC wadda za ta samar da guraben ayyukan yi ga matasa, zai bunkasa tattalin arzikin jihar da kuma kasa baki daya.
Ya ce: “Kafa tashar ruwan ta kan tudu a Maiduguri zai kawo damammaki da dama ga gwamnati da mutanen Jihar Borno .
“Wannan ci gaba zai samar da aikin yi, kuma zai rage yawan gararambar da dubban yara kanana ke yi kan titi wadda hakan na da matukar muhimmanci.
“Jihar Borno ta haɗa iyaka da ƙasashe uku, wato Nijar, Chadi da Kamaru wadda tashar jiragen ruwa ta cikin gida za ta inganta kasuwancin kan iyaka.
“Wannan shi ne abin da muke nema yadda dangantakar da ke tsakanin kasashenmu na kan iyaka za ta inganta, tattalin arzikin kasa zai bunkasa sosai, kuma GDP (kididdigar abin da Nijeriya ke samarwa) namu zai karu.
“Muna ƙoƙarin ɗauke hankalinmu daga dogaro da hanyar tattalin arzikin ɗaya, wato man fetur, ta hanyar saka hannun jari a wasu damammaki. Ina ganin Nijeriya za ta yi kyau nan ba da jimawa ba.”
Gwamnan ya ci gaba da cewa, “Gwamnatin Tarayya na ƙoƙarin ganin an gyara layukan dogo a ƙarƙashin shirin Shugaban Kasa Bola Tinubu na habaka tattalin arzikin kasa.”
A cewarsa a halin yanzu, “Gwamnatin Tarayya na kan aikin gyara dukkan hanyoyin, kuma dubban manyan motoci na shiga Maiduguri kullum.”
“A yanzu tashar ruwa ta kan tudu wadda za ta taimaka matuƙa a cikin ƙasa. Muna sa ran za a ƙarasa aikin nan da watanni shida.”
A nasa ɓangaren, Babban Sakataren hukumar ta NSC, Pius Akutah ya bayyana cewa, idan aka kafa tashar jirgin ruwa ta kan tudu a Maiduguri, za ta bunkasa harkokin cinikayyar kan iyaka, duba da cewa Borno na makwabtaka da ƙasashen Kamaru, Chadi da Jamhuriyar Nijar.