Taron shekara-shekara na fasahar sadarwar zamani kan makomar nahiyar Afirka karo na uku zai gudana a ranar 19 ga watan Nuwamba 2020.
Gagarumun taron, a bana zai gayyato masu ruwa da tsaki sama da 3,000 daga bangarorin rayuwa daban-daban, kama daga masu zuba jari, kwararru a harkar fasaha, ‘yan siyasa, fitattun mutane da dai sauransu da nufin lalubo hanyoyin bunkasa nahiyar.
Sanarwar da masu shirya taron suka fitar dauke da sa hannun Shugaban Kwamitin Tsare-tsare, Staniel Tetteh, ta ce taron na 2020 kamfanin GSE da hadin gwiwar Google cloud da AWS da IBM Cloud da Hubspot da Sendgrid da PointGlobal da ma wasu da dama ne suka daukin nauyin gudanar da shi kuma zai gudana ne ta intanet.
Sanarwar ta ce taron zai gudana ne daga karfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na yamman ranar Alhamis 19 ga watan Nuwamba, 2020.
Mahalarta taron sukan tattauna matsalolin da ke ci wa nahiyar Afirka tuwo a kwarya tare da kirkiro hanyoyin amfani da fasahar zamani wajen magance su.
Masu gabatar da kasidu da makaloli yayin taron sun hada da wakilai daga fitattun jaridu da mujallu na duniya irinsu Forbes da Bloomberg da Wired da TechCrunch da sauransu.
Sanarwar ta kuma ce masu son daukar nauyin taron ko ba da gudunmuwa na iya tuntubar masu shirya taron ta adireshin e-mail [email protected] domin karin bayani.
A baya dai, fitattun mutanen da suka yi jawabi a taron sun hada da Shugaban Gidauniyar Africa Rising Ndaba Mandela, Tom Davies na mujallar Forbes, Ty Health na kamfanin sadarwa na LinkedIn da Dakta Yetunde Odugbesan-Omede na kamfanin Google da dai sauransu.