A ranar Laraba, 20 ga watan Janairun 2021 ne aka rantsar da Joe Biden na jam’iyyar Democrat a matsayin Shugaban Amurka na 46, wanda ya ci gajiyar Donald Trump, Shugaban Amurka na 45 dan jam’iyyar Republican.
A watan Afrilun bara Biden ya ayyana kudirin tsaya wa takarar Shugaban Kasar Amurka, inda a ranar 18 ga watan Agusta jam’iyyarsa ta Democrats ta tsayar da shi a matsayin dan takarar tare da mataimakiyarsa Kamala Harris.
- Gobara ta tashi a masana’antar rigakafin COVID-19
- Mutum 3 sun gurfana a gaban kotu kan laifin tayar da zaune tsaye
- ’Yar Sarkin Kano Muhammad Sanusi I ta rasu
Biden da Kamala sun lashe zaben Amurka da aka gudanar a ranar 3 ga watan Nuwamba, inda suka tika Donald Trump da Mike Pence da kasa da rinjaye mai girma.
An haifi Joseph Robinette Biden Jr. a ranar 20 ga watan Nuwamban 1942 a Asibitin St. Mary da ke yankin Scranton a Jihar Pennsylvaniya ta kasar Amurka.
Shi ne dan da iyayensa, Catherine Eugenia Biden (Jean) da Joseph Robinette Biden Sr. mabiya addinin Kirista na Katolika suka fara haihuwa.
Yana da ’yan uwa ta suka fito ciki daya da suka hadar da mace daya mai suna Valerie, da kuma maza biyu; Francis da James.
Mahaifiyarsa Jean da kuma mahaifinsa, Joseph Sr. wanda ya kasance Bafaranshe da ya yi gudun hijira zuwa Birtaniya, duk sun fito ne daga yankin Ireland.
Biden ya yi karatu a Jami’ar Delaware da ke Newark inda ya yi digiri a fannonin Tarihi da Siyasa a shekarar 1965 gabanin ya samu shaidar kammala wani karatun na digiri a fannin aikin Lauya daga Jami’ar Syracuse a shekarar 1968.
A ranar 27 ga watan Agustan 1966 ne Biden ya auri matarsa ta farko bayan ta nasarar gamsar da iyayenta da suka nuna rashin amincewa a kan auren dan darikar Katolika, Neila Hunter, wadda suka yi karatu tare a Jami’ar Syracuse.
An daura auren nasu a wani Cocin Katolika na Skaneateles da ke Jihar New York, kuma sun haifi ’ya’ya uku tare; Joseph R Biden (Beau), Robert Hunter Biden da Naomi Christina Biden (Amy).
Bayan kasancewar Biden dan Majalisa a Karamar Hukumar Newcastle na tsawon shekaru biyu, an kuma zabe shi a matsayin dan Majalisar Dattawa daga Delaware a jam’iyyar Deomcrats a shekarar 1972, kujerar da ya rike har zuwa lokacin da aka zabe shi a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a shekarar 2008 tare da Shugaba Barack Obama, har zuwa 2016.
A shekarar 1972 ne Biden ya lashe zaben kujerar Sanatan mazabar Delaware, inda a ranar 18 ga watan Dasimba na shekarar, makonni kadan bayan zaben, matarsa Neila da diyarsa Amy mai shekara daya kacal a duniya suka mutu a wani hatsarin mota yayin da suka fita siyayyar bikin Kirsimeti.
Wannan lamari ya sanya Biden ya yanke shawarar ajiye aiki domin ya ci gaba da kula da ’ya’yansa maza biyu da suka tsallake rijiya da baya a hatsarin, sai dai Sanata mai rinjaye a wancan lokaci, Mike Mansfield ya shawarce shi a kan kada ya yi hakan.
Beau Biden ya zama Alkalin Sojojin Kasa a Iraki, inda daga bisani ya zama Lauyan Koli na Delaware, kuma ajali ya katse masa hanzari a shekarar bayan ya yi fama da cutar daji ta kwakwalwa.
Hunter Biden bai ba da shawarwai a kan harkokin kasuwanci da zuba hannun jari a Washington, babban birnin kasar Amurka.
A shekarar 1975 ne Biden ya hadu da matarsa ta biyu, Jill Tracy Jacobs, wacce ita ma malamar makaranta ce kamar matarsa ta farko, inda a ranar 17 ga watan Yunin 1977 aka daura musu aure a Cocin Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York.
A ranar 8 ga watan Yunin shekarar 1982, Biden da Jill suka haifi ’yarsu daya rak, Ashley Blazer, wacce ta yi aiki a matsayin Babbar Darakta a Ma’aikatar Shari’a ta Delaware daga shekarar 2014 zuwa 2019.