Duk wani abu da za a fadi game da Musulunci yana samuwa ne sakamakon aiko da Shugabanmu Annabi Muhammad (SAW), wanda kuma aiko shi rahama ce ga daukacin halitta da duk wani abu mai rai da marar rai. Wannan ne ya sanya marubucin wannan littafi na tarihisa Malam Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa ya sanya wa littafinsa sunan: TARIHIN FARIN JAKADA domin dimbin alheran da aiko shi ya zo da su. Daga yau zuwa abin da Allah Ya hukunta za mu fara gabatar da wannan tarihi. Da fatan za mu amfana shi.
Shimfida
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa da wadanda suka biyo bayansa da kyautatawa, har zuwa ranar Tashin Alkiyama.
Bayan haka, wannan littafi ne kan tarihin fiyayyen halitta, Shugaban Manzanni kuma Annabin karshe, Annabi Muhammad dan Abdullahi, (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi). Insha Allah a cikin littafin za mu fara ne daga rayuwa kafin aiko Annabi (SAW) zuwa shekarar giwaye. Za mu dubi dangartakar tsatsonsa zuwa kakan Annabawa Annabi Ibrahim (AS). Daga nan mu kai ga haihuwar Farin Jakada, cikakken sunansa, nasabarsa, tasowarsa har zuwa aiko shi. Za kuma mu kawo rayuwarsa a Makka da hijirasa zuwa Madina da yake-yakensa. Za mu kawo halayen Manzon Allah (SAW) da mu’amalarsa da zamantakewarsa a tsakanin al’umma. Har ila yau littafin zai duba mu’ujizojinsa da rayuwarsa da iyalansa da muhimmancin salati a gare shi da nuna masa soyayya da bin umurninsa. Za kuma mu kawo wafatinsa da abin da ya biyo baya.
Hakika sanin tarihin Manzon Allah (SAW) yana da matukar muhimmanci da fa’ida mai yawa ga kowa. Kadan daga cikin fa’idojin da ke cikin sanin tarihinsa (SAW) akwai:
Karanta tarihin Annabi (SAW) ibada ce.
Sanin tarihin Annabi (SAW) na koyar da tarbiyya ga mutane.
Karanta tarihin Annabi (SAW) na dauwamar da son Annabi (SAW) a zuciya.
Ana tabbatar da gaskiyar kyawawan halayensa da rayuwa abar koyi daga sanin tarihinsa (SAW).
Da wannan tarihi za mu ga tsarkakakkiyar nasabarsa da irin raino da tsarin rayuwa mai ban mamaki da Allah Ya taso da shi a kanta.
Tarihin Annabi (SAW) yana fito da gagarumin aikin da aka yi wajen yada addinin Musulunci tun a farkonsa da gudunmawar da sahabbai masu daraja suka bayar da sadaukarwa da muminan farko suka yi a farkon Musulunci.
Tarihin Annabi (SAW) na kara fito da fassarar ayoyi da hadisai masu yawa, kuma hanya ce ta koyon ibada da yadda ake neman kusanci ga Allah.
Tarihin Annabi (SAW) na kara kishin addini da jarunta wajen kare martabar addini. Kuma a koyi bin tafarki mafi inganci na sadaukar da kai don kare addinin Allah.
Tarihin Annabi (SAW) yana koyar da jagoranci da iya tafiyar da mulki da tausaya wa masu rauni da taimakon gajiyayyu da mulki na adalci da rikon amana.
Tarihin Annabi (SAW) yana sa wa zuciya natsuwa da kamala da farin ciki, yana maganin matsaloli masu yawa da dan Adam zai iya shiga a rayuwarsa ta hanyar ganin darussa da abubuwan misalai masu kawo maslaha ga dukan kalubale.
Tarihin Annabi (SAW) yana koyar da kyawawan dabi’u da halaye na girma da dattaku da karimci da kyauta da yafe laifi da hakuri da duk wata hanya ta samun rayuwa mai dadi a duniya da Lahira.
Tarihin Annabi (SAW) yana kara wa kowa riko da sahihiyar akida ta kadaita Allah da kara imani da Annabi (SAW).
Ta hanyar sanin tarihin Annabi (SAW) za a gano yadda ake cin nasara a gwagwarmaya ko akasin haka da nuna juriya da hakuri a rayuwa.
Tarihin Annabi (SAW) zai koyar da mu yadda ake fuskantar al’amura masu wuya da sarkakiya idan sun bijiro a tsakanin jama’a. Za mu koyi yadda ake cizawa a hura da gano wuraren rauni da wuraren karfi a cikin rayuwar al’umma.
Tarihin Manzon Allah (SAW) yana koyar da sahihiyar akida da cusa kyamar shirka da bidi’a a zukatan Musulmi. Tarihin Annabi (SAW) yana samar da ilimi mai amfani da kara kwadayin neman ilimi. Haka nan akan kara fahimtar ilimin shari’a da koyon addini sahihi.
Tarihin Annabi (SAW) yana fito da tarihin saukar Alkur’ani da mu’ujizozinsa da falalar karatun Alkur’ani. Tarihin Annabi (SAW) yana koyar da zaman aure da hanyar kyautata wa juna tsakanin ma’aurata da yadda ake soyayya da tausaya wa juna a zaman aure.
Tarihin Annabi (SAW) yana koyar da yawan ibada da cusa kwadayin bauta wa Allah dare da rana a zukatan bayi. Tarihin Annabi (SAW) yana koyar da kyautata wa juna da zaman makwabtaka da nisantar cutar juna a mu’amalolin kasuwanci da zaman majalisa da yin sulhu a tsakanin al’umma.
Darasi na daya
Yaya duniya ke ciki kafin aiko Annabi Muhammad (SAW)?
Hakika duniya ta kasance cikin duhun Jahiliyya kasancewar an dauki lokaci mai tsawo ba tare da Allah (SWT) Ya aiko wani Manzo mai kira zuwa kadaita Shi wajen bauta ba, kafin zuwan fiyayyen halitta. Annabi Isa (AS) ya kasance Annabin da ya zo gabanin aiko da Annabi Muhammad (SAW). Kuma bayan dauke Annabi Isa (AS), duniya ta yi dogon zama, na fiye da shekara dari shida, babu wani Manzo da Allah (SWT) Ya aiko domin kira zuwa ga addininSa.
Dadewar da duniya ta yi babu wani Manzo mai gargadi, ya jawo komawa zuwa ga salo da nau’o’i daban-daban na bautar gumaka da rayuwa irin ta dabbobi, na mai karfi ya tauye marar karfi da rashin alkibla a zamantakewa, wato rayuwa irin ta ba umarni babu hani, babu hukunce-hukunce babu shari’a. A takaice dai babu abu da duniya ta sanya a gabanta sai yake-yake da mamayar kasashe. Sai alfahari da kabila da zuriya da dangi a tsakanin mutane. Ana rayuwa babu manufa sai tafka barna da bin al’adu na maguzawan Jahiliyya.
A wancan lokaci, akwai dauloli masu karfi a sassa daban-daban na duniya, irin su daular Girkawa da ta Rumawa da ta Farisawa da ta Indiyawa da ta mutanen Sin (China) da kabilun Larabawa – wadanda duk suka shahara wajen yake-yake da mulki da kasuwanci a tsakaninsu.
Wasu daulolin irin na Rumawa suna da’awar bin addinin Annabi Isa (AS) da suka rada wa suna addinin Kirista, amma tuni sun gurbata shi tare da canja dokoki da hukunce-hukuncen da ke littafin Injila, domin su tafi da zamaninsu. Sun shigar da tatsuniyoyi da son zuciyar shugabanninsu na wancan lokaci don biyan bukatun masu mulkinsu. Wasu dauloli kuma irin su Farisa bautar wuta suke yi, kuma ba su da wani tsari na hukunce-hukuncen zamantakewa irin su tsarin auratayya ko kasuwanci da makamantansu. Haka akwai daulolin maguzanci a bangaren Indiya da mutanen China. Kuma ga kabilun Larabawa wadanda suka auka wa bautar gumaka irin wadanda mutanen Annabi Nuh (AS) suka rika wajen bauta wato kamar su Wadd da Suwa da Yaghusa da Ya’uka da Nasra da sauransu. Akwai kuma wasu gumaka da suka kirkiro irin su Lata da Uzzah da Manata wadanda suka warwatsa a cikin al’ummomin Larabawan da ke kewaye da Makka. Akwai kuma mabiya addinin Yahudu a yankunan Sham da Bagdad da wasu daulolin Hijaz.
Za a iya samun Malam Aliyu Muhammad Sa’id, Gamawa ta +2348023893141
Email: [email protected]