✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Tarihin da aka kafa a gasar cin kofin Afirka ta bana

A jibi Lahadi 8 ga watan Fabrairun da muke ciki ne za a rufe gasar cin kofin Afirka ta bana da ke gudana a kasar…

A jibi Lahadi 8 ga watan Fabrairun da muke ciki ne za a rufe gasar cin kofin Afirka ta bana da ke gudana a kasar Ekuatorial Guinea, sai dai duk da an fitar manyan kasashe irin su Kamaru da Mali da Aljeriya da sauransu daga gasar amma an kafa sabon tarihi.

Daga cikin sabon tarihin da aka kafa a gasar akwai: kasar Ghana ce ta farko a tarihin gasar cin kofin Afirka da ta kai matakin kusa da na karshe (Semi-Fainal) sau biyar a jere. Ghana ta kai matakin kusa da na karshe ne a shekarar 2008 da 2010 da 2012 da 2013 da kuma a 2015.
Sannan an kafa tarihin zura kwallaye 61 daga lokacin da aka fara gasar zuwa matakin kwata-fainal abin da ya sa ya dara na gasar da ta gudana a Afirka ta Kudu a shekarar 2013e bayan an zura kwallaye 51 a matakin kwata-fainal.
Sannan a karon farko an zura kwallaye 16 a wasannin kwata-fainal tun bayan gasar da ta gudana a shekarar 2008.
Sannan kasar Dimokuradiyyar Kongo ta kafa tarihi bayan ta fanshe kwallaye biyu da aka zura mata a raga amma ta farfado daga bisani kuma ta doke Kongo da ci 4-2 a karshen wasan. Rabon da a samu irin haka tun a gasar da ta gudana a shekarar 1070 a lokacin da Kamaru ta doke Kwaddebuwa da ci 3-2, bayan Kwaddebuwa na gaba da ci 2-0 a farkon rabin lokaci. Sannan a shekarar 1998 kuma Dimokuradiyyar Kongo ce ta farfado daga kwallaye ukun da Burkina Faso take cinta, kuma ta fanshe sannan ta samu nasara a karshen wasan a bugun fanariti. Haka kuma irin haka ta sake faruwa a shekarar 2000 a lokacin da Masar ta doke ta Burkina Faso da ci 4-2 baya Burkina Faso ce take kan gaba da ci 2-0 kafin a tafi hutun rabin lokaci. Sai kuma a shekarar 2010 inda Mali ta farke ci hudun da Angola ta yi mata, kuma ta samu nasara a karshen wasan.