✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Hamsin da daya: Sanya rabo ga doki cikin kayan ganima. Malik ya ce: “Ana rabon ganima ga doki na yaki ko da kuwa…

Babi na Hamsin da daya:

Sanya rabo ga doki cikin kayan ganima. Malik ya ce: “Ana rabon ganima ga doki na yaki ko da kuwa ba dokin da ba na Larabawa ba ne. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Dawaki da alfadarai da jakuna domin ku hau su…” (k:16:8).  Rabon ganima ga doki daya ake bayarwa ga mai shi ban da fiye da haka.

551. An karbo daga Ubaidullahi dan Isma’il ya ce: “Daga Abu Usama daga Ubaidullah daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa, “Lallai Manzon Allah (SAW) ya sanya ga doki rabo biyu, daya ga mai shi (yana nufin daga dukiyar ganima).”

Babi na Hamsin da Biyu: Wanda ya kora dabbar wani lokacin yaki:

552. An karbo daga kutaiba ya ce: “Sahlu danYusuf ya ba mu labari ya ce, daga Shu’aba daga Abu Is’hak ya ce: “Wani mutum ya ce wa Barra’u dan Azib (Allah Ya yarda da su), shin ko kun gudu daga Manzon Allah (SAW) a Ranar Yakin Hunain? Ya ce: “Na’am, amma Manzon Allah (SAW) bai gudu ba.” Abin da  ya faru saboda kabilar Hawazin sun kasance wadanda suka iya harbi, don haka farko da muka kai musu hari suka karye (gudu). Sai Musulmi suka rika dibar ganima, sai suka fuskance mu da harbin kibau, amma duk da haka Manzon Allah (SAW) bai gudu ba. Kuma lallai ni na gan shi yana bisa alfadararsa fara. Kuma lallai Abu Sufiyan yana rike da akalarta Annabi (SAW) yana cewa: “Ni ne Annabin babu karya (ba karya ba ne), ni ne dan Abdulmuddallib.”

Babi na Hamsin da Uku: Sanya sirdi da likkafa ga dabba:

553. An karbo daga Ubaidullahi dan Isma’il ya ba ni labari ya ce: “Daga Abu Usama daga Ubaidullahi daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su) daga Annabi (SAW) cewa: “Lallai shi ya kasance idan ya shigar da kafarsa cikin likkafa, taguwarsa ta tsaya (mike) da shi, a tsaye sai ya yi ihrami daga Masallacin Zul-Hulaifa.”

Babi na Hamsin da Hudu: Hawan doki (godiya) ba tare da sirdi ba:

554. An karbo daga Amru dan Aunu ya ce: “Hammad ya ba mu labari daga Sabit daga Anas (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Annabi (SAW) ya fuskance su bisa taguwarsa (godiyarsa) mara sirdi, na rataye da takobinsa bisa wuyarsa (kafadarsa).”

Babi na Hamsin da Biyar: Doki mara sauri:

555. An karbo daga Abdul’a’ala dan Hammad ya ce: “Yazid dan Zuria’u ya ce, Sa’id ya ba mu labari ya ce: “Daga kattada daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai mutanen Madina wata rana sun firgita. Sai Annabi (SAW) ya hau wani dokin Abu dalha mai saibi. Da ya komo ya ce, “Lallai na samu dokin nan naka mai sauri kamar kogi.” Daga nan kuma bai sake gudun nan ba.

Babi na Hamsin da Shida: Tsere a tsakanin dawaki:

556. An karbo daga kabusatu ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Ubaidullahi daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su),. Ya ce: “Annabi (SAW) ya shirya tsere a tsakanin dawakin da aka kiwata daga Hafya’u zuwa Saniyyat Alwada’u. Kuma ya shirya tsere a tsakanin dawakan da ba a kiwata ba, daga Saniyyat zuwa Masallacin kabilar Zuraik.” dan Umar ya ce: “Ni na kasance daga cikin wadanda suke tseren.” Abdullahi ya ce “Sufiyan ya ba mu labari cewa: “Nisan da ke tsakanin Hafya’u da Saniyyat Wada’u kamar mil shida. Amma abin da  ke tsakanin Saniyyat da Masallacin kabilar Zuraik mil daya ne.”

Babi na Hamsin da Bakwai: Muhimmacin kiwata dawaki domin tsere:

557. An karbo daga Ahmad dan Yunus ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi (Allah Ya yarda da shi),. Ya ce: “Lallai Annabi (SAW) ya sanya tsere a tsakanin dawaki wadanda ba a kiwata ba, nisan tserensu kamar daga Saniyyat zuwa Masallacin kabilar Bani Zuraik. Kuma lallai Abdullahi dan Umar ya kasance yana daga cikin wadanda suke tsere a cikinta.” Abu Abdullahi Bukhari ya ce: “ Amaddu na nufin kaiwa matukar nisan abu, saboda haka Allah Ya ce; “Zamanin ya yi nisa a kansu…”