✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Saba’in da Takwas: Kwadaitarwa game koyon harbin kibiya domin yakin daukaka kalmar Allah. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ku yi musu tattali gwargwadon…

Babi na Saba’in da Takwas:

Kwadaitarwa game koyon harbin kibiya domin yakin daukaka kalmar Allah. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ku yi musu tattali gwargwadon ikonku na karfi da tattalin kiwata dawaki domin ko tsoratar da makiya Allah makiyanku…..” (k:8:60).

584. An karbo daga Abdullahi dan Maslamata ya ce: “Hatim dan Isma’il ya ba mu labari daga Yazid dan Ubaidullah ya ce: “Na ji Salmatu dan Akwa’u (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya shude da wasu jama’a daga kabilar Aslam suna wasan koyon harbin kibiya. Sai Annabi (SAW) ya ce: “Ku yi harbi kabilar Isma’il domin lallai babanku ya kasance maharbi ne. Ku yi harbi ni ina tare da kabilar su wane.” Sai dayan jama’ar nan biyu suka kame hannaye su, suka bar harbi (saboda ya ce, yana tare da wadancan). Manzon Allah (SAW)ya ce: “Me ya hana muku harbi? Suka ce, “Don me za mu yi harbi alhali ka ce, kana tare da su (wane)? Sai Annabi (SAW) ya ce: “To! Ku yi harbi ina tare da ku gaba dayanku.”

 

585. An karbo daga Abu Nu’aim ya ce: “Abdurrahman dan Ghasil ya ba mu labari daga Hamza dan Abu Usaid ya ce, daga babansa ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “A ranar Yakin Badar lokacin da muka yi sahu ga kuraishawa su ma suka yi muna sahu. Idan suka yi kusa daku, to, ku dame su da harbin kibau.”


Babi na Saba’in da Tara: 

Wasanni da makami (masu) don koyo da makamancinsu:

586. An karbo daga Ibrahim dan Musa ya ce: “Hisham ya ba mu labari daga Ma’amar daga Zuhuri daga dan Musayyib daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Wata rana mutanen Habasha suna wasanni a wurin Annabi (SAW) da makamansu. Sai Umar ya shigo ya debi tsakuwa ya watsa musu. Sai (Annabi) ya ce: “kyale su ya Umar!” Aliyu ya kara da cewa Abdurrazak ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ce: “Wasan a cikin Masallaci suka yi shi.”

   

Babi na Tamanin: 

Kariya da garkuwa da bayanin hukunci mutumin da ke amfani da garkuwan abokinsa:

587. An karbo daga Ahmad dan Muhammad ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Auza’iyyu ya ba mu labari daga Is’hak dan Abdullahi dan Abu dalha daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Abu dalha ya kasance tare da Annabi (SAW) yana kariya (tsare musu harbin abokan gaba) da garkuwar guda. Saboda Abu dalha ya kasance wanda ya kware wajen harbi ne. Sai ya kasance idan ya yi harbi sai Annabi (SAW) ya daukaka (mike) wajen kallon wurin da kibiyarsa ke harbi.”

588. An karbo daga Sa’id dan Ufair ya ce: “Yakub dan Abdurrahman ya ba mu labari daga Abu Hazim daga Sahlu ya ce: “Lokacin da kwalkwali da ke kan (shi) Annabi (SAW) ya fasa masa kai jini ya rufe fuskarsa. Aka karya hakoransa na gaba, don haka Aliyu ya kasance yana debo ruwa a cikin garkuwa Fadima tana wanke masa jinin. Lokacin da ya ga jinin na karuwa bisa ruwan sai ya tafi ya debo tabarman kaba aka kona ya rika likawa bisa rauninsa jinin ya tsaya.”

589. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Amri daga Zuhuri daga Malik dan Ausu dan Hadasan daga Umar (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Dukiyar ganima da aka samu daga wajen kabilar Bani Nadir dukiya ce da Allah Ya bayar da ita ga ManzonSa (SAW) wanda ba Musulmi ne suka yi kokarin samo ta ba da dawakansu ko wadansu mahaya. Saboda haka wannan dukiya ta kasance kebance ga Annabi (SAW), domin ya kasance yana ciyar da iyalansa abincin shekara, abin da  ya saura sai ya sanya shi ga sayen makamai da dawaki don tattalin daukaka kalmar Allah.”

590. An karbo daga kabusatu ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Sa’ad dan Ibrahim ya ce, Abdullahi dan Shaddad ya ba ni labari ya ce: “Na ji Aliyu (Allah Ya yarda da shi), yana cewa: “Ban taba jin Annabi (SAW) yana sanya iyayensa fansa ga rayuwar wani mutum ba face Sa’ad (dan Abu Wakkas ba) na ji shi (Annabi) yana cewa: “Yi harbi mahaifina da mahaifiyata fansa ne gare ka.”