✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na dari da Sittin da daya: Rera waka a yakin daukaka kalmar Allah da bayanin daukaka murya a lokacin tonar ramin Khandak (gwalalo). A…

Babi na dari da Sittin da daya:

Rera waka a yakin daukaka kalmar Allah da bayanin daukaka murya a lokacin tonar ramin Khandak (gwalalo). A cikin wannan ruwaya akwai Sahlu da Anas daga Annabi (SAW), ya kara daga Yazid daga Salmata. 

708. An karbo daga Musaddad ya ce: “Abul Ahawas ya ba mu labari ya ce, Abu Is’hak ya ba mu labari daga Barra’u dan Azib (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Na ga Manzon Allah (SAW) a ranan tonar Khadak (gwalalo) yana tonar kasa har kura ta rufe gashin kirjinsa. Saboda shi ya kasance mai yawan gashi a lokacin yana rera wakar Abdullahi cewa:  

 Ya Allah! Ba domin Kai ba da ba mu shiryu ba 

* Da ba mu yi sadaka ba da ba mu yi Sallah ba. 

 Allah! Ka sanya natsuwa gare mu 

* Ka tabbatar da duga-duganmu in mun hadu.  

 Lallai abokan gaba sun zalunce mu 

* Duk lokacin da suka nemi fitina kanmu sai mu ki. 

Yana daukaka muryarsa da ita. 

 

Babi na dari da Sittin da Biyu: Wanda ya bai tabbata bisa doki: 

 709. An karbo daga Muhammad dan Abdullahi ya ce: “dan Numair ya ba mu labari ya ce, Idris ya ba mu labari daga Isma’il daga kais daga Jarir (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) bai taba tsare ni wajen ganinsa ba, tunda na Musulunta. Kuma bai taba ganina ba face ya yi murmushi a fuskarsa. Hakika na kai kuka zuwa gare shi cewa: “Lallai ni ban tabbata bisa doki sai ya bugi kirjina da hannunsa ya ce: “Ya Allah Ka tabbatar da shi bisa doki, Ka sanya shi mai shiryarwa abin koyi.”

 

Babi na dari da Sittin da Uku:

Maganin rauni shi ne a kona tabarmar kaba. Da hukuncin ’ya mace za ta iya wanke wa babanta jini daga fuskarsa da debo ruwa cikin garkuwa. 

710. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Abu Hazim ya ba mu labari ya ce: “Sun tambayi Sahlu dan Sa’ad Sa’idiyyu (Allah Ya yarda da shi), cewa: Ko da me aka yi wa Manzon Allah (SAW) maganin rauninsa? Sai ya ce: “Babu wanda ya saura cikin mutane wanda ya fi ni sani. Aliyu ya kasance yana deian ruwa a cikin garkuwarsa Fadima (AS) tana wanke masa jini daga fuskarsa. Sai aka samo tabarmar kaba aka kona, sa’an nan aka rufe ciwon (raunin) Manzon Allah (SAW).”

 

Babi na dari da Sittin da Hudu:

Abin da aka hana game da jayayya da sabani cikin yakin daukaka kalmar Allah. Da bayanin hukunci wanda ya saba wa shugabansa. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Kada ku rika jayayya sai ku rarraba karfinku ya tafi…”(k:8:46). Abin da ake nufi kada a saba a lokacin yaki.

711. An karbo daga Yahya ya ce: “Waki’u ya ba mu labari daga Shu’abah daga Sa’id danAbu Burdatu daga Babansa daga Kakansa cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya aika Mu’azu da Abu Musa zuwa garin Yamen sai ya ce musu: “Ku saukaka, kada ku tsananta, Ku rika bushara kada ku rika kore jama’a. Ku rika yi wa juna biyayya kada ku yi sabani (a tsakaninku).”

 

Imel: [email protected]