Babi Na Shida: Babu wasiyya ga mai gado:
445. An karbo daga Muhammad dan Yusuf ya ce: “Daga Warka’u daga dan Abu Najih daga Adda’u daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Dukiya ta kasance ga da ne, wasiyya kuma ta kasance ga iyaye biyu. Sai Allah Ya shafe haka da abin da Ya so kuma Ya sanya wa namiji rabon mata biyu. Ya sanya wa iyaye biyu kowane daga cikinsu na da kason daya cikin shida. Ya sanya wa mace kason daya cikin takwas, ko daya cikin hudu. Miji kuma na da rabo ko kason daya cikin hudu.”
Babi na Bakwai: Sadaka lokacin mutuwa:
446. An karbo daga Muhammad dan Ala’u ya ce: “Abu Usama ya ba mu labari daga Sufiyan daga Imarah daga Abu Zur’ata daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Wani mutum ya ce da Annabi (SAW) ya Manzon Allah! Wace sadaka ce ta fi laheri? Ya ce: “Ka yi sadaka lokacin da kake da lafiya kana mai kwadayin dukiyar. Kana tattalin dukiya, kana tsoron talauci. Kada ka yi jinkiri har lokaci da rai ke kaiwa ga makoshi.” Ka ce, “Na ba wane kaza, wane kuma na ba shi kaza, kuma hakika na ba wane kaza.”
Babi na Takwas:
Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Bayan wasiyya da aka yi wasiyya da ita ko bashi…”(k:4:11). An ambata daga Shuraih da Umar dan Abdul’aziz da dawus da Adda’u da dan Uzainatu sun halatta furucin mara lafiya bisa ga bashin da ya ce ana bin sa. Alhassanul Basari ya ce: “Mafificin abin da mutum zai yi sadaka da shi a karshen yininsa na duniya, da farkon yininsa na karshe (lokacin mutuwarsa, shi ne wasiyya).” Ibrahim da Alhakam sun ce: “Idan mai jinya ya barrantar da mai gado game da bashin (sa) to mai gado ya barranta.” Rafi’u dan Khadijah ya yi wasiyya kada a bude matarsa Alfazariyya ga abin da duk aka rufe kofarta a kansa (wato babu mai tarayya da ita a cikin gidanta).” Alhassan ya ce: “Idan mutum ya ce, wa bawansa lokacin mutuwa: Ni na kasance zan ’yantaka, to haka ya halatta.” Shu’uba ya ce: “Idan mace ta ce, lokacin mutuwarta lallai mijina ya biya ni bashina kuma na karba, ya halatta.” Wadansu mutane sun ce: “Furucin majinyaci ba ya halatta saboda zai haifar da mummunan zato daga masu gado, sa’an nan suka kyautata (yarda) da furucinsa bisa ga ajiya da kayan sautu da abin da aka yi alkawarin raba riba.” Saboda lallai Annabi (SAW) ya ce: “Kashedinku da aiki da zato domin zato shi ne mafi karyar magana.” Kuma dukiyar mutum Musulmi ba ta halatta bisa fadar Annabi (SAW) cewa: “Alamar munafiki idan an amince masa sai ya yi ha’inci.” Da fadar Allah Madaukaki cewa: “Hakika Allah Yana umurtarku da bayar da amanoni zuwa ga mazowanta…”(k:4:58). Bai kebance mai gado ba ko waninsa.” Wadanda suka yarda da wannan fatawa akwai Abdullahi dan Amru daga Annabi (SAW).”
447. An karbo daga Sulaiman dan Daud Abu Rabi’u ya ce: “Isma’il dan Ja’afar ya ba mu labari ya ce, Nafi’u dan Malik dan Abu Amir Abu Suhail ya ba mu labari daga babansa daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce: “Alamar munafiki guda uku ne: Idan ya yi magana zai yi karya. Idan aka amince masa ya yi yaudara. Idan ya yi alkawari ya saba.”
Babi na Tara:
Fassarar fadar Allah Madaukaki cewa: “Bayan wasiyya da aka yi wasiyya da ita, ko bashi…” (k:4:11). An ambata daga Annabi (SAW) cewa: “Ya yi hukunci da biyan bashi kafin wasiyya.” Da fadar Allah Madaukaki cewa: “Hakika Allah Yana umurta da a bayar da amanoni zuwa ga mazowanta…” (k:4:58). Bayar da amana ya fi cancanta daga sadakar wasiyya. Annabi (SAW) ya ce: “Babu sadaka face bisa bayyanar wadata.” danAbbas ya ce: “Bawa bai wasiyya face da iziini shugabanninsa.” Annabi (SAW) ya ce: “Bawa mai kiwo ne cikin dukiyar shugabansa.”